Babbar cibiyar nan mai rajin kawo sauyi a Nigeria, ( Concern For Better Nigeria), tare da hadin gwiwar World Islamic Funds ,sun rage kaso 30 çikin 100 na farashin kayayyakin abinci don saukakawa al’umma.
Cibiyar CFBN ta yi ragin ne don al’umma su Samu rahusa sakamakon gabatowar watan azumin Ramadan.
Cibiyar Concern for better Nigeria, karkashin jagorancin Alhaji Kabiru Abubakar , ya ce kayayyakin da suka yi rangwamen kaso 30 çikin 100 na farashin su, sun hada da Shinkafa, Taliya, Makaroni, Manja, Man gyada, Masara, Dawa, Gero da Wake.
Haka zalika akwai Doya, Dankali duka dai don Samun falala da albarkar azumin Ramadan.
Cibiyar CFBN tana maraba da dukkan al’umma, a ofishin su dake lamaba 15 AMG Plaza kwanar Garin Gurungawa Bay Pass karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano.
Ko kuma a tuntube su ta nambobin waya kamar haka 08023040660, 09160663534 Concern for better Nigeria ( CFBN) taken mu shi ne muhadu mu gina kasar mu.