Ina matuƙar farin cikin kasancewa cikin wannan muhimmiyar tattaunawa da aka shirya, wadda aka yi wa lakabi da “Daga Titi Zamu Gyara – Kawar da Matsalar Ƴan Daba a Jihar Kano.” Ina taya A. A. Zaura Foundation murna da mika godiya ta bisa wannan gagarumin yunkuri na gyara da sauya rayuwar matasan da suka fada tarkon daba zuwa masu amfani da gina al’umma.
2. Fadan daba da shaye-shaye na daga cikin manyan kalubale da ke fuskantar jihar Kano. Duk da irin ƙoƙarin da hukumomin tsaro ke yi, dole ne mu haɗa kai domin fuskantar wannan matsala. Rundunar ƴan sanda ta Jihar Kano tana ganin cewa shigar da al’umma da masu ruwa da tsaki yana da matuƙar muhimmanci wajen samun zaman lafiya da cigaban ƙasa.
3. Tun bayan da na karɓi ragamar jagorantar Rundunar Ƴan Sanda a Kano, watanni biyu kenan daidai, na gudanar da bincike tare da nazarin yanayin laifuka a fadin jihar. Daga abinda na samu, ya bayyana karara cewa wajibi ne mu mayar da hankali musamman kan laifukan Fadan Daba da kuma shaye-shaye. Wadannan matsaloli suna matukar barazana ga zaman lafiya da makomar matasanmu.
4. A kokarin kawo karshen wadannan matsaloli, mun ƙirƙiro tsari na musamman da ya dace da umarnin Babban Sufeto Janar na Ƴan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM, dangane da dabarun ‘community policing’. Ta hanyar haɗin gwiwa da al’umma, gudanar da sintiri, haɗaka da sauran hukumomin tsaro, tara bayanai na sirri, da amfani da fasahar zamani, mun kama mutane dari uku da hamsin da bakwai (357) da ke da hannu cikin fadan daba, miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan tashin hankali. Mun kuma kwato bindigogi, makamai masu haɗari, miyagun ƙwayoyi da dukiyoyin da aka sace waɗanda ke ƙarfafa yaduwar laifuka a tsakanin al’ummar mu.
5. Duk da cewa wadannan nasarori abin farin ciki ne, ina mai jaddada mana cewa yanzu muka fara. Tushen wannan matsala na daba da shaye-shaye yana da alaka da matsalolin zamantakewa, rashin aikin yi, da kuma ƙarancin kulawa da tallafi ga matasa. Babu shakka, shirye-shirye irin wannan za su ba wa matasa madadin rayuwa mai kyau tare da kawo sauƙi ga tsaro da zaman lafiya a Jihar Kano.
6. Wannan shirin na dauke matasa daga tituna ba tare da amfani da karfi ba, yana da matuƙar kyau, kuma ya dace da manufofinmu na ƙarfafa ‘community policing’ da rage aikata laifuka. Muna da yakinin cewa gyaran hali da ba da dama ga matasa abubuwa ne muhimmai wajen magance matsalolin da ke haddasa daba da shaye-shaye.
7. Yayin da muke tattaunawa a kan hanyoyin da za su zama masu ɗorewa da samar da haɗin gwiwa, ina kira da mu muyi duba zuwa abubuwa kamar haka:
• Dabaru da hanyoyin dogaro da al’umma wajen gyaran hali da tallafawa matasa
• Haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da kungiyoyin fararen hula.
• Samar da ayyukan yi da ƙarfafa tattalin arzikin matasan da ke cikin haɗarin afkawa miyagun laifuka.
• wayar da kan jama’a domin inganta kyawawan dabi’u da ingatacciyar rayuwa
8. Ina da tabbacin cewa wannan hadaka zata haifar da kofar samun mahimmiyar tattaunawa da shawarwari masu amfani. Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Kano za ta ci gaba da bada cikakken goyon baya ga wannan yunkuri. Muna fatan yin aiki tare domin kawo ƙarshen dabanci da shaye-shaye a Jiharmu.
9. Na gode.