Cikin Hotuna: An yi addu’ar musamman ta neman sauƙin matsin rayuwa a Kano

Spread the love

Duk da kiraye-kirayen da aka rinƙa yi na neman a ɗage addu’o’i na musamman da aka tsara za a fara yi daga yau Asabar a Najeriya, bayanai sun nuna cewa an gudanar da addu’ar a masallacin, gidan Isiyaku Rabi’u da ke Goron Dutse, a yankin, ƙaramar hukumar Dala, da ke Kano.

Jaridar daily Trust ta ruwaito cewa, wani mai amfani da shafukan sada zumunta da muhawara a sanya a shafinsa na Facebook cewa: ”Ana karatun Qur’ani daga nan masallacin Khalifa Isyaku Rabiu, Goron Dutse, Kano, domin addu’a kan halin da kasarmu ke ciki, Allah Ya sawƙaƙa mana, Amin.”

Daman jaridar ta ruwaito cewa ɗaya daga cikin mutanen da suka shirya addu’ar ƙasa da za a fara yau Asabar 10 ga watan Agusta, 2024, a masallacin na Isiyaku Rabi’u, da kuma sauran jihohin ƙasar, Mubarak Ibrahim Lawan, ya sanar da cewa an fasa saboda dalilai na tsaro.

Ganin yadda zanga-zangar lumana da aka fara a Najeriyar ranar 1 ga watan nan na Agusta ta tsawon kwana goma ta rikiɗe a wasu jihohin ƙasar ta zama tarzoma inda aka inka sace-sace da ɓarnata dukiya ta gwamnati ta ‘yan kasuwa da sauransu, har ma da kisa da raunata jama’a, wanna ya sa wasu suka yi, tunanin karkata ga addu;a domin samun sauƙi a kan matsalolin da ke addabar ƙasar.

A wani saƙo na bidiyo da ya fitar, a Kano, Mubarak, ya ce kwamishinan ƴansanda na jihar, da kuma darektan hukumar tsaro ta DSS shi ma na jihar sun ankarar da su cewa wasu ɓata-gari a ƙasar sun shirya tura wasu miyagu wajen taron addu’ar, domin cimma manufarsu.

Ya ce, an yi zargin cewa za su jagoranci wasu matasa da za su riƙa kwashe kayan jama’a da na hukuma, da sace-sace, kamar yadda aka yi a baya a lokacin da aka fara zanga-zanga, a saboda haka ya ce sun fasa taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *