Cikin Hotuna: Gwamnatin Kano Ta Kaddamar Da Kyautar Motocin 78 Ga Rundunar Yan Sandan jahar

Spread the love

Gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya godewa jami’an Yan Sandan jahar, kan yadda suka jajirce wajen gudanar da aiyukan su dare da rana.

Gwamnan ya bayyana hakan hakan ne, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa ya yin da kyautar motoci guda 78 ga jami’an Yan Sandan jahar Kano, ranar Talata.

Taron dai ya a fadar Gwamnatin jahar kamar yadda Jaridar idongari.ng, ta ruwaito.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce kwamishinan yan Sandan jahar CP Salman Dogo Garba, ya Yi wa Gwamnan alkawarin yin Aiki da motocin da aka basu yadda yakamata.

CP Salman Dogo, ya kara da suna ofisoshin baturen Yan Sanda guda 78 , area commands 11, da kuma Outpost guda 100.

Haka zalika Gwamnatin Kanon , ta ce Yan Sandan sun sadaukar da rayuwarsu don ci gaba da tabbatar da tsaro a fadin jahar.

Saurari muryar Gwamnan jahar Kano Engr Abba Kabir Yusuf..

Tuni dai aka kaddamar da bayar da motoci kirar Hilux guda 44 ga baturen Yan Sanda na kananan hukumomin Kano, ya yinda ragowar motoci guda 34 kirar Sharon za a kammala sanya mu su na’urori Kafin kaddamar da su.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *