Cikin Hotuna: Rundunar Yan Sandan Kano Ta Cafke Matasa Sama Da 100 Da Ake Zargi Da Satar Kayan Mutane.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano ta kama wasu daga cikin matasan da ake zargi da fasa shagunan al’umma da kuma barnata kayan gwamnati, tare da wawashe kayan baki daya.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani takaitaccen sako da ya wallafa a shafin sa na facebook tare da hotunan matasan da ake zargi da aikata laifin.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Nigeria suka fito kan titina a jahohin kasar don bayyana wa gwamnati halin matsin rayuwar da suke ciki , sakamakon sauye-sauyen gwamnatin tarayya ciki harda cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi a ranar 29 ga watan Mayu 2023.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce an kama wadanda ake zargin sama da 100 a wurare daban-daban kuma za su sanarwa da jama’a halin da ake ciki anan gaba.

‘’ Wannan abun da akeyi ba zanga zanga bane, ya koma satar kayan mutane’’ SP Abdullahi haruna kiyawa’’.

Tuni dai Gwamnan jahar Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da sanya dokar hana fita a faɗin jihar tsawon a wanni 24

Gwamnan ya kuma umarci jami’an tsaro su tabbatar kowa ya bi wannan doka, wadda aka kafa bayan wasu ɓata-gari sun koma fasa shaguna da gine-gine yayin zanga-zangar matsin rayuwa da aka fara gudanar wa a fadin Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *