Cikin Hotuna Yadda Aka Ci Gaba Da Harkoki A Kano.

Spread the love
Kano

Harkokin yau da kullum sun ci gaba da gudana a sassan birnin Kano, kamar yadda aka Saba a koda yaushe ba tare da Wata fargaba ba.

A Ranar Lahadin da ta gabata wasu gungun Matasa wadanda Suka fito daga masarautun da aka rushe , inda Suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu.

Haka zalika wasu masoyan sarkin Kano na 15 sun gudanar zanga-zangar, akan Titin zuwa gidan Gwamnatin jahar Kano, har aka kona Tayoyi .

A Daren jiya Lahadi ne Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya ce sun gano yunkurin da wasu batagarin Mutane ke Yi, na bankawa majalissar dokokin jahar Kano wuta da sauran wurare don tayar da hankali al’ummar jahar.

CP Usaini Gumel, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Daren jiya Lahadin , inda ya bayar da tabbatacin cewar al’umma su kwantar da hankulan su, kuma su ci gaba da gudanar da harkokin yau da kullum kamar yadda aka Saba, domin sun baza jami’an tsaron su a sassa daban-daban na jahar.

Zuwa wannan lokaci motocin jami’an Soji da na yan sanda ne ke bayar da kariya a gidan Sarki na Nasarawa, sai dai babu fitowar jama’a daidai lokacin muke hada wannan rahoto, amm an Samu Karin jami’an tsaron yan sanda kamar yadda Wakilin mu na ganewa idonsa.

A fadar mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sunusi na ii , kuwa akwai tsirarun Mutane da suke zuwa don ta ya shi, murnar samun sarautar gidan Dabo a matsayin sarki na 16.

A Ranar 9 ga watan Maris 2020 ne tsohon gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya cire sarki Munahammadu Sanusi ii, daga kan kujerarsa bayan kirkirar sabbin masarautu guda 4 a shekarar 2019, wanda  majalissar dokokin jahar ta wancan lokacin ta yi.

To sai dai majalissar dokokin jahar Kano ta yanzu , ta Yi wa dokar masarautun gyaran fuska, inda ta rushe Karin masarautun , Rano , Gaya, Karaye da kuma Bichi, inda gwamna ya sanya hannu tare da cire sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, tare da Mayar da gurbinsa da Muhammadu Sunusi na ii.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *