An ɗaura auren wasu ‘yan mata marayu fiye da 100 a garin Bungudu na jihar Zamfara.
Dukkanin ‘yan matan dai waɗanda suka rasa iyayensu ne sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa kan ƙauyuka a jihar.
Dan majalisar wakilan yankin, Hon. Abdulmalik Zubairu Bungudu – wanda ya ɗauki nauyin ɗawainiyar auren – ya shaida wa BBC cewa tuna ya tanadi kayan ɗaki da jari da aka raba wa amaren a lokacin bikin.
An dai raba wa amaren kayan ɗaki da suka ƙushi gado da katifa da kujeru da sauran kayayyakin ɗaki
”A lokacin bikin kowace amariya za mu ba ta jarin naira 100,000 yayin da kowane ango kuma zai samu naira 50,000 a matsayin tallafi.
Hon. Bungudu ya ce an bi matakai kafin zaɓo marayun, inda aka ware wa kowacce mazaɓa marayu biyar da za su amfana da tsarin.