A jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, an samu tsirarun mutane da suka fito zanga-zanga a rana ta biyar da fara ta a sassan kasar.
Duk da cewa an sanya dokar hana fita a jihar, amma an tsinkayi wasu matasa na zanga-zanga a wasu yankunan birnin.
An dai sanya dokar takaita zirga-zirga a fadin jihar bayan da aka samu hatsaniya, to amma gwamnatin jihar ta sassauta dokar daga karfe 8 na safe zuwa 2 na rana.
Sai dai kuma bankuna sun kasance a rufe amma akwai na’urar ATM da ke aiki a wasu bankunan.
Manyan kasuwannin sun kasance a rufe.
Masu baburan a dai-daita suna zirga-zirga amma gidajen mai da dama duk sun kasance a rufe.
Jami’an tsaro kuma na ci gaba da kasancewa a mahimman wurare don dakile abin da ka iya tasowa.
Ga hotuna daga wasu sassan birnin na Kano a yau Litinin:
Yadda masu zanga zanga suka fito a jihar Legas
A rana ta biyar da fara zanga zanga a Najeriya, masu zanga zangar sun sake fitowa kan titunan jihar Legas.
Ga hotunan yadda zanga zangar ta yau ta kasance.
Tinubu ya tabbatar a wani jawabi da aka watsa a fadin kasar a ranar Lahadin da ta gabata cewa gwamnatinsa a shirye ta ke ta saurare da kuma magance matsalolin masu zanga-zangar, yana mai tabbatar da cewa ya ji kiran nasu da babbar murya