Cikin Hotuna Yadda Aka Kara Wa Jami’an Yan Sandan Kano 11 Girma.

Spread the love

Jami’an Yan Sandan jahar Kano, 11 ne suka Samun girma zuwa mataki na gaba, Wanda hukumar kula da aiyukan Yan Sanda ta kasa PSC, ta Yi , a ranar 2 ga watan Satumba 2024.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labari a jiya Alhamis.

Cikin wadanda suka samu karin girman sun hada da DCP Abdu Sabo, a matsayin mukaddashin kwamishinan Yan Sanda, sai Haliru Ibrahim da Mohammed Chindo Usman , a matsayin mataimakan kwamishinan yan Sanda.

Sauran sune wadanda suka samu girman daga SP zuwa CSP, da suka hada da Bashir Tijjani, Raubilu Ubayi Ringim, Abubakar Ado, Kabiru Bello, Mohammed Ibrahim Aga, Amiru Lawan, Dahiru Lawan da kuma Abdulmalik Ibrahim.

Da yake gabatar da jawabin sa kwamishinan yan Sanda jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya taya wadanda suka samu karin girman murna, tare da kira a gare su da kara hazaka wajen gudanar da aiyukan su.

A jawabin sa na godiya Daya Daga cikin wadanda suka samu karin girman DCP Abdu Sabo, ya godewa hukumar PSC, Kwamishinan Yan Sandan Kano da sauran al’ummar da suka halacci taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *