Al’ummar garin Sabon Birni a jihar Sokoto sun gudanar da sallar janazar Sarkin Gobir na Gatawa, Isa Bawa da safiyar yau Alhamis, bayan kashe shi da ƴan bindiga suka yi.
Labarin kisan sarkin ya ɓulla ne a ranar Laraba, bayan da bayanai suka tabbatar da cewa ƴan bindigar sun halaka shi duk da neman kuɗin fansa da suka yi.
Ɗaruruwan mutane ne suka hallara domin gudanar da sallar a garin Sabon Birni.
Kisan basaraken na zuwa ne bayan ya shafe sama da mako uku a hannun ƴan bindigar waɗanda suka ɗauke shi a kan hanyarsa ta zuwa wani taro.
Tuni shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya miƙa ta’aziyya ga iyalai da kuma masarautar ta Gobir, tare da yin alƙawarin kawo ƙarshen matsalar tsaro a yankin.
Sokoto na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar ƴan fashin daji masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha iƙirarain cewa tana bakin ƙoƙarinta wajen magance matsalar, sai dai har yanzu abin bai yi sauƙi ba a wasu sassan ƙasar.
Jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto, Neja da Kaduna na cikin jihohin da matsalar ta fi yin ƙamari.