Cikin Hotuna : Yadda Kwamitin PCRC Na Area Command Eastern Bypass Kano Ya Rantsar Da Sabbin Shugabanni

Spread the love

Shugaban kwamitin aikin tsaro da al’umma (PCRC) na Area Command eastern bypass, Nura Ali Bayero, ya yi kira ga al’umma da su riƙa tallafawa Hukumomin tsaro musamman ‘yan sanda, don samar da ci gaba wajen tabbatar da zaman lafiya.

Nura Ali Bayero , ya bayyana hakan ne lokacin da ake ƙaddamar da shugabannin kwamitin tsaro da Al’umma( PCRC) na ofisoshin Baturen ‘yan sanda da kuma Area command ta Eastern Bypass.

Suma wasu daga cikin yan kwamitin PCRC sun bayyana kudirin su wajen bayar da gudummawa ga jami’an ‘yan sanda ta kowanne bangare.

 

Haka zalika an karrama mataimakin kwamishinan yan sandan Kano, mai kula da Area Command ta Eastern Bypass, ACP Abdullahi Kambe .

 

Sauran wadanda aka karrama da lambar yabo sun hada da, CSP Abdul Ya’u Sadik baturen yan sandan Phanshekara, CSP Bilyaminu Bello baturen yan sandan Na’ibawa, CSP Kabiru Bello baturen yan sandan Dawakin Kudu, CSP Sani Garba baturen yan sandan Dorayi Babba da kuma SP Mustapha Kebbe baturen yan sandan Kumbotso.

Taron ya gudana ne a area command ta Eastern Bypass dake garin Danmaliki karamar hukumar Kumbotso.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *