Al’ummar unguwar Gayawa a yankin karamar hukumar Ungoggo Kano, sun gudanar da zanga-zangar lumana bisa halin rashin hanyoyi da suke Yi mu su barazana.
Idongari.ng, ta ruwaito cewa dubban mutane ne suka fito tare da Daga Kwalaye ma su dauke da rubuce-rubuce a jiki domin Kai kokensu ga mahukunta don su share mu su dauki.
Haruna Musa Isma’il , ne ya jagoranci tawagar mutanen, domin bayyana wa gwamnati halin da suke ciki, kan rashin hanya wadda ta ke kawo koma baya a yankin.
” Muna cikin kakanikayi , ruwa ya ruwa Yana Yi mana barazana” Haruna Musa “.
Haruna ya ce idan sun dawo daga Kasuwa suna fuskantar matsaloli na rashin koma gida akan lokaci, Inda suka bukaci gwambatin jahar Kano, ta samar mu su da hanyar.
A cewar su tunda aka fara mulkin Demokuradiya suke ta kokawa Amma har yanzu ba a kai Yi mu su ba.
Haka zalika mutanen Gayawan sun Yi kira ga Yan majalissun su na tarayya da na Jiha, su waiwaye su Bisa alkawarin da suka Yi a baya.
Titinan da suke bukatar gyaran sun hada da titin na Tsahare, Jaba, Gayawa , Titin Badaru da kuma Rimin Kebe.
Rashin kan hanyoyin ya kawo koma baya kan abunda ya shafi kasuwanci, lafiya da kuma ilimi.