Kwamitin bayar da Tallafi na Dan majalissar wakilan Nigeria, na kananan hukumomin, Rano, Kibiya da kuma Bunkure, RT.Hon. Kabiru Alhassan Rurum Kano, ya bayar da Tallafin kudi ga daliban dake daukar horo yanzu haka na aikin Dan Sanda , wadanda suka fito daga mazabar Dan majalissar.
Kwamitin ya mika Tallafi kudin ne a ranar Lahadi, a makarantar horas da jami’an Yan Sandan dake jahar Kaduna .
Dan majalissar wakilan RT.Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ta Hannun kwamitin bayar da Tallafin sun Yi fatan Alkairi ga daliban Yan Sandan.