Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki don wayar da kan al’umma kan abunda ya shafi harkar tsaro.
Taron dai an gudanar da shi ne, a ranar Asabar 12 ga watan Oktoba 2024, a Sani Abacha Youth Center, kuma an shirya Taron ne don karkafawa hukumomin tsaro gwiwa da kuma ba su goyon bayan da yakamata tare da kara kulla alaka Tsakanin Yan Sanda da jama’a.
Cikin wadanda suka kasance a Taron masu ruwa da tsakin, sun hada da Hakimai, Dagatai, masu unguwanni , yan kwamitin aikin tsaro da al’umma PCRC, Yan Sandan Sarauniya, Bijilanti da sauran sun hada da Unguwannin, Na’ibawa, Kumbotso, Phanshekara , Ja’en, Sharada, Dorayi, Danbare, Rijiyar Zaki , Dawakin Kudu da sauran hanyoyin da za su hada Kano zuwa Kaduna ko jahar Katsina.
Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce Taron ya haifar da da Mai Ido, domin an samu Kwararrun da suka wayar da kan al’umma don cigaba da Sanya idanu a unguwanni tare da Sanarda jami’an Yan Sanda duk wani motsi da ba su amince da shi ba.
kwamishinan yan Sandan jahar Kano , CP Salman Dogo Garba, Wanda Area commander na Eastern Bypass, ACP Bello Hamisu Wudil, ya wakilta, ya nuna farin cikinsa da yadda aka gudanar da taron.
Sauran wadanda suka bayar da gudunmawa, a wajen Taron sun hada da , Ambassador Muktar Gashash , Dagacin Sharada Alhaji Iliyasu Mu’azu, SP Umar Sa’id Abdullahi daga sashin tattara bayanan sirri na shelkwatar Rundunar Yan Sandan Kano.
Kwamishinan Yan Sandan jahar , ya ba wa baturen Yan Sanda da mataimakan kwamishinan na shiyoyin jahar, da su hada irin wadannan taruka da al’ummar su, don tattauna Abubuwan da za su kawo ci gaban tsaro.
Rundunar Yan Sandan ta ce an samu gagarumin ci gaba , domin aikata laifuka a jahar ya ragu sosai.
An dai tattauna matsaloli da dama da kuma hanyoyin magance matsalar.