Sanatan Kano ta Arewa, a majalissar dattawan Nigeria, Sanata Barau I. Jibrin, ya kaddamar da baburan aikin sintiri guda 1,000 ga rundunar yan sandan jahar, don kara fadada sintiri a lungu da sako.
Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ne ya bayyana hakan, ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya godewa Sanata Barau jibrin, bisa kokarin da yake yi akoda yaushe kan abunda ya shafi harkar tsaro a fadin jahar
‘’ Dole sai kara godiya agare shi, bisa namijin kokari da yake yi, tabbas a shekarar da ta gabata kunga motocin da ya bayar guda 22, inda raba su a ofisoshin yan sanda na shiyar Kano ta arewa’’ cewar SP Abdullahi Kiyawa’’.
Ya kara da cewa baburan da Sanatan ya bayar dukkansu sababbi ne, kuma suna shelkwatar rundunar yan sandan Kano.
Saurari muryar SP Abdullahi Haruna Kiyawa
Idan ba a manta ba jaridar www.idongari.ng, ta ruwaito mu ku yadda Sanata Barau, ya bayar da kyautar motoci guda 22 ga rundunar yan sandan Kano, a ranar 17 ga watan Febarairun 2023.
Da yake gabatar da jawabinsa mataimakin shugaban majalissar Datttawan Nigeria, sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Sanata Barau I Jibrin, ya ce wajibi ne a yaba wa jami’an yan sandan Kano, da kuma sauran hukumomin tsaro, kan yadda suka tsayin daka wajen tabbatar da tsaro.
Barau ya kara da cewa, dukkan shiyar arewa maso yamma babu inda yakai jahar Kano samun zaman lafiya, sakamakon samun jajirtaccen kwamishinan yan sanda CP Salman Dogo Garba.
‘’ muna gode mu ku gabaki daya, shi lamari na rayuwa idan Allah ya yi maka baiwa, Sai kamanta da cewar baiwa ce, amma ba zaka tuna ba sai tuna sauran abubuwan da suke faruwa a makota kamar sauran jahohi, amma a kano babu yan ta’adda, masu garkuwa da mutane kuma babu duk wata rigima muna zaune lafiya wannan abune na Allah saboda addu’ar da ake yi wa yan sandan da sauran hukumomin tsaro’’Barau I Jibrin.
- Sojojin Sama Sun Kashe Yan Bindiga Sama Da 100 A Katsina
- IPOB: Najeriya na so a miƙa mata Simon Ekpa
Sanatan ya ce wajibi ne kowa ya taimaka mu su domin harkar zaman lafiya da tsaro ba ta gwamnati ce ita ka dai ba, ko yan sanda, DSS da Civil defence da sauransu harka ce ta kowa da kow.
‘’ kowa sai ya taimaka, da Malamai, Attajirai, Dalibai harma talakan da yake yawo akan titi shima ya bayar da tasa gudunmawar wajen bayar da labarin wadanda suke son kawo matsala’’.
Ya kuma ce daman ya yi alkawarin dukkan wani jami’in dan sanda da yake aiki a Kano ta arewa, sai ya mallaki baburin hawa don gudanar da aiki, harma ya sake alkawarta cewa nan da watanni biyu ma su zuwa sai kaddamar da wasu sabbin baburan ga jami’an yan sandan dake aiki a Kano ta Tsakiya sannan aje Kano ta Kudu.
‘’ don haka duk wani mai aikata laifi ya daina domin, idan abaya yana gani jami’an yan sanda mota ce kawai da su , ba za su iya shiga wasu wuraren ba, to yanzu za su shiga ko ina lungu da sako.
Saurari muryar Sanata Barau I Jibrin…….
Ya kuma kara da cewa sai kara samar da kayan sadarwa jami’an yan sandan bayan ya kammala bayar da Baburan.
Sai dai ya koka kan yadda wasu ke kalubalantar jami’an yan sandan cewar sun kaza, inda ya mayar da martani da cewar ba su da kayan aikin da yakamata ne, amma idan aka samar mu su za a ga aiki da cikawa.
Rundunar yan sandan jahar Kano, ta kara kira ga masu hannu da shuni da sauran al’umma da su taimakawa harkar tsaro.
‘’ wannan abu da aka yi zai kara mana kwarin gwiwa’’.