Cikin Kwanaki 4: Kwamitin Magance Fadan Daba, Shaye-shaye Ya Kama Shahararrun Dalolin Kwaya Da Yan Daba 31

Spread the love

 

Kwamitin tsaron da gwamnatin jihar Kano ta kafa don magance fadace-fadacen daba da ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma gyara tarbiyar matasa, karkashin jagorancin Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata, ya kai sumame wuraaren da ake zargin maboyar yan Daba ne da kuma dilolin miyagun kwayoyi, a unguwannan Dorayi, Ja’en, Sharada, Unguwar Dabai, Dukawa, Kabuga, Kofar Mata da makotan unguwannin, daga ranar 10 zuwa 14 ga watan Mayun 2025.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aikewa da manema labarai, a ranar juma’a.

Sanarwar ta ce an kai sumamen ne biyo bayan samun sahihan bayanan sirri , a inda batagarin suke taruwa , inda aka kama mutane 31, wadanda 25 daga cikinsu ake zargi da laifukan daba sai kuma mutane 6 da ake zargi da dillacin miyagun kwayoyi.

Kayayyakin da kwamitin tsaron ya kwato sun hada da, bindigar Harbin tsintsaye 4, wukake 9, Adduna, Gorori 3 sinki-sinki na tabar wiwi guda uku da rabi sai kuma kwayar Exol 173 da dai sauran miyagun kwayoyi.

Cikin wadanda aka kama harda shahararrun yan daban unguwar Dorayi, da suka hada da, Dan Abba, Baka Kashi, Ramos, Abba Maciji da kuma Abdul Baki dukkansu yan shekaru 25, kuma tuni an gurfanar da su a gaban kotun majistiri mai lamba 16 dake zamanta a Zangeru Road , inda kotun ta bayar da umarnin tsare su a gidan yari, yayin da sauran mutanen 6 cikinsu harda fitaccen mai dillancin kwayoyi ,Rabi’u Hamza, an mika su hannun hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA reshen jihar Kano don fadada bincike kafin a gurfanar da su a gaban kotu.

Wannan dai wata nasara ce a kokarin da ake yi don magance daba kuma shaye-shaye a sassan jihar Kano

Kwamitin wanda ya kunshi gamayyar hukumomin tsaron Kano da wakilan gwamnatin Kano don tsaftace jihar daga aikata laifuka da kuma wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma.

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *