Cikin Wata Guda: Rundunar Yan sandan Kano Ta Cafke Mutane 120 Da Ake Zargi Da Aikata Laifuka Maban-banta.

Spread the love

Rundunar Yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar cafke Mutane 120, da ake zargi da aikata laifuka maban-banta daga Ranar 1 zuwa 31 ga watan Maris 2024.

Kakakin rundunar Yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Ranar juma’a.

Sanarwar ta kara da cewa , samun nasarar zuwa ne bayan daukar matakan yaki da Masu aikata munanan laifukan a fadin jahar.

Wadanda rundunar Yan sandan jahar Kano, ta cafke sun hada Masu garkuwa da Mutane 4, Yan fashi da makami 15, Dilolin Kwaya 10 da kuma barayin ababen hawa su 14.

Sauran sune wadanda ake zargi da aikata laifukan Damfara 2, Barayi 20 sai kuma Yan Daba 55 da ake zargi da addabar mutanen wasu sassan jahar.

Yan sandan sun yi nasarar kubutar da Mutane 3 da aka yi garkuwa da su, tare da kwato harsasan bindigar AK47 guda 15, Bindigu kirar gida 24, Motoci 7, Adaidaita sahu 3, Babura ma su kafa biyu 5, wukake 28, Adduna 10 da Danbida 7.

Sauran kayan da aka kwato sun hada da, Tumaki 45, Jarkokin Manja 15, Wayar wutar lantarki da kuma Atamfofi guda 347.

Kwamishinan Yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya tabbatar wa da al’ummar jahar cewa za su Ci gaba da kare rayukansu da dukiyoyinsu, a koda yaushe.

A karshe SP Abdullahi Kiyawa, ya ce da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da su a gaban kotu dan su fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *