Cikin Watanni 8 Al’ummar Bauchi ta Kudu Sun gamsu da wakilcin mu :Sanata Shehu Buba Umar.

Spread the love

Sanatan Mai wakiltar yankin Bauchi ta Kudu Sanata Shehu Buba Umar ya bayyanna cewar tuni al’ummar yankinsa suka Gamsu da wakinsa a kasa da watanni 8 da zabarsa domin ya wakilci yankin Bauchi ta Kudu a Majalisar Dattawa.

Sanatan ya bayyanna hakan ne a gana wa da wakilin idongari.ng, Kabiru Muhammad Getso a gidansa dake cikin Garin Bauchi, ya ce tun a watan farko ya fara cika alkawarikan da ya dauka lokacin yakin neman zabe.

Daga cikin Ayyukan da ya fara sun hada da Samar da Katafariyar makarantar horar da jami’an yaki da fasa kwauri ta kasa a yankin nasa sannan bada jimawa ba ya samarwa matasa da dama aiyukan yi a matakin Gwamnatin Tarayya Sannan ya bijiro da tsarin Tallafawa Mata da matasa da tallafin Jari don suyi sana’oi don dogara da Kansu.

Karan ta wannan labarin Ana neman wadanda suka fitar da dala miliyan shida da sa-hannun bogi na Buhari

Karan ta wannan labarin Kotu ta tisa keyar Murja Ibrahim Kunya gidan gyaran hali a Kano

“Wani abun da ke farantawa al’ummar yankin shi ne yadda ya ware kowanne karshen wata domin baro Abuja yazo yankin nasa domin ganawa da Mutanen nasa Wanda hakan wani sabon abu ne da al’ummar yankin basu saba ganin hakan ba” Inji shi.

Sanata Shehu Buba ya kara da cewar akwai kuduri masu matukar Mahimmanci da ya gabatar a Majalisa Wanda da zarar ya tsallake to babu shakka al’ummar yankin nasa dama Jihar Bauchi zasu dara matuka, Bangaren Ilimi ma Sanatan yayi kyakkyawan Tsari domin Bunkasa sha’ainin ilimin tun daga matakin Firamare har zuwa na gaba da sakandire don tallafawa al’ummar yankin nasa

Sanata Shehu Buba ya yabawa daukacin al’ummar jihar Bauchi Musamman na yankin Bauchi ta kudu bisa irin Gwarin Gwiwa da goyon da suke bashi don cigaba da bijiro kyakkyawan Ayyukan da zai amfanesu

Ya ce duk da shi kadai ne mai Babbar Kujera Daga Jam’iyyar APC a Jihar Bauchi amma hakan bai hana shi kula da ‘yan Jam’iyyar ba domin tallafa masu a koda yaushe don rage radadin rayuwar da ake ciki,sannan ya shwarce su da su cigaba da bashi goyon baya domin nan bada dadewa ba al’umma zasu kara fahimtar irin kyakkyawan tanadin da akai ma su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *