Ƙungiyar Ɗaliban Najeriya (NANS), ta shaida wa Shugaba Bola Tinubu cewa matsalar man fetur na ƙara ta’azzara a Najeriya, kuma cire tallafin bai haifar da ci gaban da ake tsammani ba.
NANS, ta ce cire tallafin ya jawo matsaloli masu yawa ga ’yan Najeriya kuma ya haifar da ƙarancin man fetur maimakon wadatarsa.
Sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Abdul-Yekinn Odunayo, magatakardar ƙungiyar, ya fitar a Abeokuta a ranar Asabar.
“NANS tana matuƙar damuwa game da tsadar mai da kuma ƙarancin man fetur da ake fama da shi a ƙasar nan. Cire tallafin man fetur ya jawo wa ’yan Najeriya wahala mai tsanani, matsalar man fetur ta ci gaba da ƙamari.
“Wannan matsala ba kawai tattalin arziƙi ta ke cutarwa ba, har ma tana shafar jin daɗin ɗalibai da karatunsu a faɗin ƙasar na. ’Yan Najeriya na fuskantar ƙalubale sosai wajen samun man fetur.
- Ana Zargin Mai Fasa Kaurin Motoci Da Hallaka Jami’in Kwastam
- Jami’an Tsaro Da Fursunoni Sun Mutu A Yunkurin Tserewa Daga Gidan Yarin Mogadishu
“Akwai dogayen layuka a gidajen mai a ko ina, duk da alƙawarin da Shugaba Bola Tinubu ya yi na cewa samun tsaikon mai zai ƙare. Amma hakan ba ta samu ba.
“Tsadar man fetur ta sa farashin sufuri ya ƙaru sosai, kuma ya haifar da tsadar kayan masarufi. Wannan tsadar na ƙara ta’azzara komai.
“Abin takaici ne cewa shekara ɗaya bayan cire tallafin, matsalar man fetur ta ƙara ta’azzara, kuma kamar ba a son ƙasar nan ta ci gaba.
“NANS na kira ga gwamnati da ta ɗauki matakan gaggawa don magance wannan matsala kafin haƙurin ’yan Najeriya ya ƙare.”