CISLAC ta yi kira a wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano

Spread the love
CISLAC

Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokoki da Yaƙi da Rashawa a Najeriyar wato CISLAC, ta bayyana matukar damuwa a game da abubuwan da ke faruwa a Kano dangane da batun sauya sarki a jihar.

CISLAC ta yi gargadin cewa irin abubuwan da ke faruwa a jihar ta Kano na barazana ga zaman lafiyar jihar.

Babban darakta a cibiyar, Auwal Musa Rafsanjani, ya fitar da tsattsauran gargadi a kan duk wani yunkuri na amfani da yanayin da ake ciki a jihar domin ayyana dokar ta baci.

Ya ce, ” Irin wadannan ayyuka ana kallonsu ne a matsayin ganganci da kuma takalar fada na babu gaira babu dalili da janyo bata shekara 1000 na tarihin siyasar jihar”.

CISLAC, ta lura cikin fargaba cewa matsayin kotun wanda hukumomin tsaro suka dogara dashi shi ne ya janyo dawowar sarki Aminu Ado Bayero mai cike da takaddama a ciki.

Sanarwar cibiyar ta ce gwamnatin jiha ce kundin tsarin mulki ya bawa damar nadi da kuma tabbatar da sarakunan gargajiya ciki har da Sarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *