Gamayyar kungiyoyin Arewacin Nigeria , wato Coalition of Northern Groups (CNG), ta ce matukar ana so a kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi Arewacin kasar, sai kowa ya ba da gudunmawar sa a harkar tsaron.
Jami’in gudanarwar gamayyar kungiyoyin na kasa kwamared Jamilu Aliyu Chiranchi, ne ya bayyyana hakan ya yin taron manema labarai da gamayyar Kungiyoyin Suka gudanar a jiya Juma’ a a jahar Kano.
- Kwamishinan Yan Sandan Kano Ya Nemi Hadin Kan Kafafen Yada Labarai Don Wanzar Da Zaman Lafiyar Jahar.
- Ramaphosa ba zai sauka daga muƙaminsa ba – jam’iyyar ANC
Ya kuma ce, taron na su ya biyo bayan zaman da su ka yi da ma su sana’ar finanan Hausa da ma su shirya wasan da kuma masu amfani da kafafan sadarwa na zamani.
Rahotanni na cewa gamayyar kungiyoyin na Arewa sun ce nan gaba kadan za su zauna da yan jarida da kuma mamallaka gidajen jaridu dangane da yadda za a shawo kan matsalar tsaron da ta addabi yankin na Arewacin Nigeria.