CP Bakori Ya Shiga Ofis A Matsayin Kwamishinan Yan Sandan Kano Na 47

Spread the love

Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya karɓi ragamar shugabanci a matsayin Kwamishina na 47 a heldikwatar rundunar dake unguwar Bompai anan kano.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin,  cewa CP Bakori ya maye gurbin  tsohon kwamishinan yan sanda, AIG Salman Dogo, da ya samu Karin girma zuwa Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda (AIG).

An haifi CP Bakori, a ranar 6 ga watan gaFabrairu, 1969 a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina, ya  shiga aikin ‘yan sanda a ranar 15 ga Agusta a  shekarar 1996 a matsayin Cadet ASP, inda ya sami horo a Kwalejin ‘Yan Sanda ta Wudil, Kano.

CP Bakori ya halarci manyan kwasa-kwasai da dama a fannin aikin ‘yan sanda, ciki har da horon aiki na Rundunar ‘Yan Sandan ,tare da tafiya-tafiye  zuwa ƙasashe fiye da 25 a Afirka, Asiya da Turai, inda ya ƙara samun gogewa a aikin ‘yan sanda na duniya.

CP Bakori ya sha alwashin yin aiki tukuru don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *