CP M.U. Gumel, Gwamna Abba K. Yusuf Sun Taya Murna Ga Yan Sandan Da Suka Samu Karin Girma A Kano.

Spread the love

Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, tare da tallafin mai girma gwamnan jahar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, sun yi bikin daga lifayar wasu jami’an yan sanda daga matsayin Duputy Superintendent of Police ( DSP) zuwa Superintendent of Police (SP).

Bikin karin girman an yi shi ne a fadar gwamnatin jahar Kano, kamar yadda mai magana da yawun rundunar yan Sandan jahar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya aike wa da jaridar idongari.ng, a ranar Laraba.

Kotu Ta Yanke Wa Mai Balle Kwanon Rufin Gidajen Jama’a Yana Mu Su Sata Hukunci.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya yi Kira ga jami’an da suka sami karin girman su sani cewar wani nauni ne, ya kara hawa Kansu, inda ya zama wajibi su kara kokaro a aiyukan su , don tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu.

Shi ma anasa jawabin gwamnan jahar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, ya taya yan sandan, da likafar ta su ta daga murna, tare da Jan hankalin su , su ci gaba da jajircewa a koda yaushe .

Wadanda suka samu Karin girman sun bayyana Farin cikin su, tare yin alkawarin, Kara kwazo, fiye da abunda suke yi, don sauke nauyin da aka dora mu su.

Sun kuma godewa Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, da gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, wadanda suka za mo cikin ma su taya su murna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *