Hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA , Reshen jahar Kano ta aikewa da kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, wasikar godiya, bisa hadin kan da yake bayarwa wajen dakile shigo wa da miyagun kwayoyi jahar.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a ranar Asabar 27/1/2024.
Duk Da Hada Layin Waya Da NIN Garkuwa Da Mutane Na Ci Gaba
Wasikar godiyar mai kwanan watan 25 ga watan Janairun 2024, mai dauke da sa hanun kwamandan hukumar yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi reshen jahar Kano, Abubakar Idris Ahmed, ne ya aike wa kwamishinan yan sandan wasikar.
Wannan na zuwa ne bayan mika wasu miyagun kwayoyi da rundunar yan sandan jahar, ta kama ga hukumar NDLEA, Don fadada bincike kan lamarin.
Wasikar ta NDLEA na cewar ta karbi tarin miyagun kwayoyin , a ranar 24 ga watan janairun 2024, daga kwamishinan yan sandan CP Muhammed Gumel.
Hukumar NDLEA ta kara da cewa, jami’an ta sun gudanar da bincika tare gano cewar kwayar Cannabis Sativa ce mai nauyin kilogram 836kg, dan haka ta na yaba wa kwamishinan yan sandan da kuma yaransa bisa kokarin da suke bayara wa , don yaki da hana sha da fataucin miyagun kwayoyin a jahar Kano.
Haka zalika kwamishinan yan sandan ya karbi nambobin gairmama wa, daga wasu kungiyoyi, ma’aikatu da sauran al’umma, kan yadda ya jajirce wajen tabbatar da zaman lafiya da kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu a jahar.
Super Eagles za ta kara da Angola bayan cin Kamaru
Kungiyoyin sun hada da , Independent Magazine Publishers Association of Nigeria , ma’aikatar Ilimi ta jahar Kano, kungiyar A A Sule Lokon Makera, Bashir Nasiru & Co, Muslim Professionals in Da’awah da kuma Awaisu Organization Gobirawa Kurna Asabe Dala da dai sauransu.
Tun zuwan kwamishinan yan sandan Kano CP Muhammed Usaini Gumel, jahar Kano a shekarar 2023, ya dakile ta’addancin yan fashin waya da yan daba da sauran laifuka a sassan Kano, wadanda a baya suka hana al’umma saket.