CP Salman Dogo Ya Gana Da Jami’an Yan Sanda Don Fadada Sintiri Da Tabbatar Da Tsaro A Kano

Spread the love

Kwamishinan yan Sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya gana da dakarun Yan Sandan da suke aikin su a jahar, Inda yaja hankalinsu a ci gaba da tabbatar tsaro da a lungu sako da fadada sintiri da kuma yin aiki kafa da kafa da al’umma da sauran hukumomin tsaro.

Cikin wata sanarwa da kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta ce kwamishinan ya gana da jami’an Yan Sandan ne a ofishin sa a ranar Litinin 19 ga watan Augusta 2024, domin ci gaba da kare rayukan al’umma da kuma dukiyoyon su.

Haka zalika ya ja hankalinsu kar ayi sake a ci gaba da tabbatar da tsaro tare da hada da al’umma , don ganin an kara Samun kyakkyawar alaka tsakanin Yan Sanda da jama’a.

Sannan a Yi Aiki Kai tsaye da sauran hukumomin tsaro don ganin an dakile duk wani Yunkuri na aikata laifuka.

SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa, za a kara fadada sintiri musamman a wanQnan lokaci don tabbatar da zaman lafiya.

” Sannan a fito cikin tsafta da kwalliya ta hanyar fadada aikin ta yadda al’umma za su fahimci aikin” SP Abdullahi Haruna Kiyawa “.

Saurari muryar kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ….

CP Salman Dogo, ya ci gaba da Jan hankali kan zama da kungiyoyi na Shugabanni da matasa da kuma wadanda za su ba da gudunmawa akan Abubuwan da suka shafi harkar tsaro.

Ya kuma bayar da umarnin a ci gaba da tattara bayanan sirri ta karkashin kasa, don inganta tsaro.

A karshe ya Yi kira ga jami’an Yan Sandan su Yi Bisa gaskiya da kwarewa kamar yadda aka horar da su , tare da gode su Bisa yadda suke aiki tukuru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *