CP Salman Dogo Ya Umarci Yan Sandan Kano Suka Kara Fadada Sintiri A Lungu Da Sako

Spread the love

Kwamishinan Yan Sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya gana da manyan jami’an Yan Sandan jahar, inda ya Umarce su da su kara fadada Sintiri a lungu da sako,don kar abar Wani batagari ya fito har ya samu damar aikata laifi a fadin jahar.

Kwamishinan yan Sandan jahar, ya gana da jami’an ne a ranar Litinin a ofishimsa dake Shelkwatar Rundunar Yan Sandan a unguwar Bompai , kamar yadda Mai magana da yawun Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya shaida wa idongari.ng.

SP Abdullahi Kiyawa, ya kara da cewa kwamishinan ya godewa jami’an Yan Sandan kan yadda suke tabbatar da tsaro a yankunansu, tare da Jan hankalin su don kar abar batagarin mutane su fito don yin Ta’addanci ko aika-aika a jahar Kano.

Haka zalika, ya kuma umarce su, da su Fita don ganawa da al’ummar su ta hanyar wayar mu su da Kai kan abinda ya shafi tsaro.

Cikin jawabin da ya gabatar , kwamishinan yan Sandan, ya ce baya son Jin labarin aikata laifi a fadin jahar, don haka wajibi ne su kara fadada Sintiri da kuma kara bude hanyoyin Samun bayanan sirri ta Hannun al’umma don ganin an tsaftace Baki daya.

A karshe ya godewa al’ummar jahar Kano, bisa hadin Kan da suke ba wa Yan Sanda ako wannan lokaci.

Saurari muryar kakakin rundunar yan sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *