CP Salman Dogo Ya Ziyarci Wuraren Da Aka Kakkabe Aiyukan Batagari, Da Inda Aka Samu Mummunan Hadarin Mota.

Spread the love

Daga Mujahid  Wada Musa.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Salman Dogo Garba, ya kai ziyara wuraren da aka gudanar da aikin kakkabe batagari, musamman a unguwannin, Sheshe da kuma kwanar Goda.

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya aike wa da jaridar idongari.ng, a Ranar Litinin 1 ga watan Yuli 2024.

Sanarwa ta Kara da cewa, Kwamishinan ya kuma Kai wata ziyarar , a yankin Dangoro kan titin Zaria road, inda aka Yi hadarin mota har mutane 25 Suka rasu, ya yin da mutane 53 suka samu raunuka.

SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ziyarar da CP Salman Dogo, ya kai ne domin bibiyar yadda yan sanda suke gudanar da Aiyukan su, musamman irin aikin Kai sumame don yin maganin batagari, da kuma gana wa da al’ummar yankin na yadda Suka ga an gudanar da aiki a wuraren.

Kwamishinan yan sandan , ya gana da da Jami’an yan sanda wadanda Suka gudanar da Aiyukan , tare da yaba mu su, kan yadda Suka Yi kokari na ganin an magance harkar Daba baki daya.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa yanzu haka an Kama mutane da ya wa, inda ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

A ziyarar Kwamishinan yan sandan zuwa wurin da aka samu hadarin mota, inda aka rasa rayuka tare da jikkatar wasu da dama, ya Yi addu’a da kuma jajantawa wadanda abinda ya shafa, da kuma Kara Kira ga Dorebobin mota su ci gaba da bin dokokin tuki, sannan a guji gudun wuce sa’a, yin lodi ba bisa ka’ida ba da kuma kaucewa gudun ganganci.

Rundunar Yan Sandan ta ziyarci wuraren ne domin ci gaba da aiki da kwarewa da kuma tabbatar da Tsaro da zaman lafiya a jahar Kano.

” Wanda kuma ya Kara jan hankalin yan sanda, da cewa shi ba zai zauna a ofis, ana aikata laifukan Daba ba , saboda haka duk Wanda ya fito da wani makami da niyyar Daba KO fitowa da niyar Yi wa mutane rauku ko kisa da kuma fashi da makami, Kwamishinan ya bayar da umarni ga yan sandan su Yi amfani da duk karfinsu domin su magance ko waya harda ma su daure mu gindi” SP Abdullahi Haruna Kiyawa “.

A karshe Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya Kara yin godiya ga al’ummar jahar , bisa gudunmawa da goyon baya da suke bayarwa a kowanne lokaci.

Sannan ya bukaci jama’a, a duk lokacin da Suka wani motsi KO hanzari, Wanda ba su amince da shi ba , su gaggauta sanarwa a ofishin yan sanda mafi kusa, don daukar matakin da ya dace.

Haka zalika za a iya kiran yan sanda akan nambobin waya 08032419754, 08123821575 da 090 29292926.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *