Ƙasashe biyar a gabashi da kudancin Afirka na fama da ɓarkewar cutar anthrax, in ji hukumar lafiya ta duniya WHO a yankin Afirka.
Sama da mutane 1100 ne ake zargin sun kamu da cutar kuma mutane 20 ne suka muta a Kenya da Malawi da Uganda da Zambia da kuma Zimbabwe – tun farkon wannan shekara.
Ƙasar Zambia dai na fuskantar bullar cutar mafi girma tun shekara ta 2011, inda larduna 9 daga cikin 10 nata suka kamu da cutar.
Yayin da cutar ke yaɗuwa a cikin dabbobi a Malawi, ƙasar ta ba da rahoton bullar cutar ta farko da aka taɓa samu a bana.
Dakta Matshidiso Moeti, darektan hukumar ta WHO a Afirka ta ce tana tallafawa wajen ƙoƙarin yaƙi da ɓarkewar cutar a faɗin ƙasar.
Ta kara da cewa “Don kawo karshen wadannan barkewar dole ne mu karya tsarin kamuwa da cuta ta hanyar fara rigakafin cutar a dabbobi,” in ji ta.
A cewar masana kiwon lafiya, ana iya haifar da ɓarkewar cutar ta hanyar abubuwa da yawa, da suka haɗa da girgizar yanayi da ƙarancin abinci da rashin fahimta da kamuwa da cutar ta hanyar kula da naman dabbobin da suka kamu da cutar.