Cutar sanƙarau ta kashe ɗalibai 20 a Yobe

Spread the love

Dalibai 20 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a makarantun sakandaren mata guda uku da kwalejin ‘yan mata ta gwamnatin tarayya da ke kananan hukumomin Potiskum da Fika a jihar Yobe.

Kwamishinan Ilimi na primary da Sakandare na Jihar Yobe, Mohammed Sani-Idris a hirarsa da BBC ya tabbatar da mutuwar ɗaliban inda ya ce 17 daga cikin ɗaliban da suka mutum ƴan makarantar kwana ne kuma ragowar mutum uku ɗin ƴan primary ne.

Kwamishinan ya kuma ce an kwantar da ɗalibai da dama a asibiti amma an sallame su.

Jagoran Lauyoyin da Ya jagoranci maka Ado Gwanja, Badamasi.S.Gandu a Kotu bayan Rera wakokin ASOSA da Chass Ya Magantu.

Gwamnatin Kano Zata Dafawa Aiyukan Hukumar Hisbah Don Yaki Da Badala A Tsakanin Al’umma.

Ya kuma ƙara da cewa shi da sauran jami’ai sun koma garin Potiskum na ɗan wani lokaci domin hana yaɗuwar cutar.

A halin da ake ciki Gwamna Mai Mala Buni wanda mataimakinsa Idi Barde-Gubana ya wakilta ya ziyarci makarantun da lamarin ya shafa domin ganin halin da ake ciki.

Gwamnan ya ce: “A wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na shawo kan cutar tare da maganceta yadda ya kamata, gwamnati ta riga ta samar da magungunan gaggawa tare da tura tawagar gaggawa zuwa dukkan yankunan da abin ya shafa”.

A asibitin ƙwararru na Potiskum kuma, an samu adadin mutane 214 da suka kamu da cutar sannan uku kuma suna cikin sashin kula da lafiya na asibitin suna karbar magani.

Irin wannan barkewar cutar ta kashe mutane da yawa mazauna yankin Degubi a karamar hukumar Fika ta jihar a watan Afrilun 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *