Da ba a cire tallafin mai ba da wahalar Najeriya ta fi ta yanzu – Gwamnatin tarayya

Spread the love

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na Najeriya, Alhaji Mohammed Idris Malagi ya ce, da gwamnati ba ta cire tallafin mai ba da wahalar da ake ciki a ƙasar ta fi haka a yanzu.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake kare matakin gwamnatin ƙasar na cire tallafin mai a yayin wata hira da tashar talabijin ta Channels.

A lokacin jawabinsa na farko bayan rantsuwa, a Abuja, a watan Mayu na 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu sauran tallafin mai.

Tun daga lokacin da shugaban ya sanar da janye tallafin man kayayyaki da sauran harkokin rayuwa a Najeriya suke ta tashin gwauron zabo, rayuwa take ta kara tsada ga jama’a.

Kafin cire tallafin man ana sayar da lita ɗaya a ƙasar a lokacin a kan naira 189 a watan Mayu, amma bayan sanarwar cirewar farashin ya koma daga naira 650 zuwa sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *