Gwamnatin jahar Kano ta bayar da umarnin cafke tsohon sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero , nan ta ke bisa zargin yunkurin haifar da rudani a jahar.
Mai magana da yawun gwamnatin jahar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa , ne ya bayyana hakan ta cikin Wata sanarwa da ya raba wa manema labarai , da safiyar a sabar.
Sanarwar ta ce tsohon sarkin ya shigo jahar cikin dare, a yunkurin sa na koma wa kan karagar mulki , bayan tsige shi da gwamnan jahar ya yi .
Sunusi Bature, ya Kara da cewa tuni sabon sarkin Kano , Muhammadu Sunusi na ii, na samu rakiyar gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakin sa Kwamared Aminu Abdussalam , da kakakin majalissar dokokin jahar Kano, da sauran mukarraban gwamnatin zuwa fadar masarautar Kano.
Gwamnan ya bai wa Kwamishinan yan sandan jahar umarnin Kama wa , tare da tsare tsohon sarkin bisa zargin kawo rudani da haifar da rashin zaman lafiya a jahar.