Da Dumi-Dumi: Za A Gurfanar Da Matashin Da Ake Zargi Da Bankawa Mutane Wuta A Gaban Babbar Kotun Musulinci A Kano.

Spread the love

Rahotanni da muke samu a yanzu haka na cewa, za a Gurfanar da matashin nan mai suna Shafi’u Abubakar, da ake zargi da yin Sanadiyar rasuwar mutane 17, bayan ya banka mu su wuta a lokacin da suke yin sallar Asuba, a wani Masallaci dake Laraba Abasawa Karamar hukumar Gezawa Kano.

Za a gurfanar da matashin a gaban babbar kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Rijiyar Zaki karkashin jagorancin mai Shari’a Halhalatul Kuza’i Zakariya.

Kakakin manyan kotunan shari’ar addinin musulinci na jahar Kano, Muzammil Ado Fagge , ne ya tabbatar da hakan.

Tun a Ranar larabar makon da ya gabata , rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta Samu nasarar cafke matashin da ake zargi da aikata laifin kunna wutar Fetur, inda mutane 24 Suka kone wadanda aka kwantar da su a, Asibitin Murtala Muhammed, inda mutane 17 daga cikin majinyatan Suka rasa rayukansu.

A jiaya ne gwamnan jahar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin daukar matakin Shari’a, kan matashin mai suna Shafi’u Abubakar, da ake zargi da bankawa jama’a wuta a lokacin da suke yin sallar Asuba, a yankin Unguwar Gadan dake Karamar hukumar Gezawa Kano, inda mutane 24 Suka kone sakamakon Iftila’in.

Gwamnan Abba Kabir, ya bayyana hakan ne lokacin da ya ziyarci asibitin kwararru na Murtala Muhammed Kano, don duba wadanda Suka gamu da iftila’in konewar.

Gwamnan ya yi Allah Wadai da yadda matashin ya Rufe jama’a suna yin sallah, sannan ya banka mu su wuta, inda ya tabbatar da gwamnati ba za ta kyale lamarin ba.

Abba Kabir Yusuf, ya nesanta batun da siyasa KO ta’addanci, kamar yadda wasu ke fada , harma ya bayyana cewa rigimar cikin gida ce ta rabon gado, sakamakon wani bai ji dadi ba, ya yanke wa kansa hukunci irin na marasa imani.

Haka zalika gwamnatin jahar Kano, ta yi alkawarin daukar nauyin jinyar wadanda Suka gamu da iftila’in kunar wutar Fetur din.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *