Da Me Shugaban Nijar Ya Dogara A Zargin Najeriya Da Faransa Da Yunƙurin Afka Wa Kasarsa?

Spread the love

Shugaban mulkin sojin Nijar Birgediya Janar Abdurrahamane Tchiani ya zargin Najeriya da Faransa da kitsa yunƙurin afka wa ƙasarsa ko yi wa Nijar bi-ta-da-ƙulli.

Cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na ƙasar, Janar Abdourahmane Tchiani ya yi zargin cewa “Faransa ta yi alƙawarin bai wa Shugaban Najeriya, Bola Tinubu wasu kuɗaɗe don kafa sansannin soji a dajin Baga, da ke jihar Borno”.

“Akwai kuɗin da suka ce za su bai wa Tinubu domin ya ba su wani wuri cikin dajin Baga a jihar Borno, wani wuri da Turawan suka yi wa laƙabi da ‘Canada’, inda suke horas da al’umomin da waɗannan yankuna”, in ji Najar Tchiani.

A cikin hirar mai tsawon sa’a guda da rabi, shugaban mulkin sojin na Nijar, Janar Tchiani ya zargi Faransa da ƙulla ƙawance da wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga a yankin Tafkin Chadi domin yi wa tsaron ƙasar Nijar zagon-ƙasa.

”Faransa ta ƙulla ƙawance da mayaƙan ISWAP da Boko Haram domin horas da su da ba su makamai da kuɗaɗe domin ta yi amfani da su wajen tayar da zaune-tsaye a Jamhuriyar Nijar”, in ji shi.

‘Faransa na da hannu a Lakurawa’

Shugaban na mulkin sojin Nijar ya ce daga bayanan da suka samu a daɗewa sun fahimci cewa na shirin kafa sansanin Lakurawa a wani daji da ke jihohin Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi.

”Wasu manyan ‘yanta’adda da muka kama, sun shaida mana cewa a ranar 4 ga watan Maris ɗin shekarar 2024, Faransa ta ƙulla wata yarjejeniya da mayaƙan ISWAP, kuma shugabannin Najeriya na sane da ita, cewa za a mayar da dajin Gaba da ke jihohin Sokoto da Zamfara da Kebbi a Najeriya sansanin horas da mayaƙan Lakurawa”, in ji shugaban na Nijar.

Janar Tchiani ya yi zargin cewa an tanadin sansanin ne domin horas da mayaƙan Lakura don su watsu a jihohin Sokoto da Zamfara da kuma jihar Kebbi da kuma jamhuriyar Nijar.

Shugaban na Nijar ya ce duk da iƙirarin mayaƙan da suka kama suka na cewa jagororin Najeriya na sane, ba su yarda da maganar ‘yan bindigar ba.

”Kan haka ne muka yanke shawarar bai wa Najeriya waɗannan bayanai, saboda ba mu yarda da jawaban na ‘yan bindigar ba, muka faɗa wa shugaban hukumar leƙen asiri ta NIA na wancan lokaci da Ahmad Rufai Abubakar, ya turo mutane cikin Nijar domin tattaunawa da ‘yan ta’addar domin tabbatar wa daga bakinsu”.

Amma daga ƙarshe a cewar shugaban Nijar, sun gwammace ba su faɗa masa wannan sirri ba, indasuka zarge shi da ɗaukar nauyin horas da ‘yan ta’adda.

”Ashe shi wannan Ahmad Rufai Abubakar da muka shaida wa wannan sirri, shi ne ke ɗaukar nauyin tura ‘yanta’adda zuwa wata ƙasa da ake kira Central Africa domin samun horo”, in ji shi.

Haka ma shugaban na Nijar ya zargi mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu da masaniya game da wannan batu.

”Duk sun san da zancen, amma suka yi shiru, tun daga nan ne muka fahimci cewa kifi tun ga kai nai ya ruɓe”.

Yayin zargin cewa an ƙuduri aniyar horas da Lakurawan ne domin su kawo tarnaƙi ga aikin bututun man ƙasar da ka shimfiɗa zuwa Jamhuriyar Benin mai makwabtaka.

Janar Tchiani ya zargi ƙasashe makwabtan Nijar da bai wa Faransa damar kafa sansanoni a ƙasashen domin horas da ‘yanta’adda da niyyar yaƙar Nijar.

A baya-bayan nan dai dangantaka tsakanin Najeriya da Nijar na ci gaba da yin tsami, ko a makon da ya gabata ma gwamnatin mulkin sojin Nijar ɗin ta zargi Najeriya da shirya mata maƙarƙashiya, kodayake gwamnatin Najeriya ta musanta zargin.

Martanin gwamnatin Najeriya

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta duka zarge-zargen na shugaban mulkin sojin na Nijar.

Cikin Hirarsa da BBC ministan yaɗa labaran ƙasar, Mohammed Idris ya ce Najeriya ba ta taɓa ƙulla wata alaƙar soji da Faransa ko wata ƙasa domin ɗaukar nauyin hare-haren ta’addanci a Jamhuriyar ta Nijar, ko tayar da zaune-tsaye a ƙasar.

Mohammed Idris ya ce shugaban Najerya Bola Tinubu a matsayinsa na shugaban Ecowas yana gudanar da jagoranci da ya kira ‘abin koyi’.

”Kuma Najeriya na iya bakin ƙoƙarinta wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma tabbatar da ɗorewar danganta mai tarihi tsakaninta da Jamhuriyar Nijar”, in ji Ministan.

Ministan yaɗa labaran na Najeriya ya ce dakarun ƙasar, tare da haɗin gwiwar dakarun ƙasashen da ke yaƙi a Tafkin Chadi na samun nasara a yaƙin da suke yi da ‘yanta’adda a yankin.

”Don haka hikima wani ya yi zargin cewa Najeriya za ta haɗa baki da wata ƙasar waje domin wargaza zaman lafiya da tsaron makwabciyarta”, in ji Mohammed Idris.

Dangane da zargin wasu jami’an gwamnatin Najeriya da Janar Tchiani na cewa suna ɗaukar nauyin ‘yantadda da ba su horo kuwa, ministan yaɗa labaran ƙasar ya ce babu ƙamshin gaskiya game da zargin.

”Gwamnatin Najeriya ko wani jami’inta ba su taɓa sanya hannu a bai wa ‘yanta’adda tallafin makamai domin kai wa Nijar hari”, in ji shi.

Haka kuma ministan ya musanta zargin bai wa Faransa wuri domin kafa sansanin.

”Najeriya ba ta taɓa bai wa wata ƙasar waje damar kafa sansanin soji a ƙasarta ba”

A nata ɓangare majalisar dattawan ƙasar – wadda yanzu hake ke hutu – ta alƙawarta gudanar da cikakken bincike kan wadannan zage-zarge, da zarar ta koma baikin aiki.

Babban mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Tahir Munguno – wanda ke wakiltar arewacin Borno, ya ce ya kaɗu da waɗannan manyan zarge-zarge da shugaban mulkin sojin Nijar ya yi kan gwamnatin Najeriya.

Cikin zantawarsa da BBC , Sanata Munguno ya ce bisa tsarin dokokin Najeriya dole idan za a kawo sansanin sojin wata ƙasa zuwa Najeriya, to dole ne sai an nemi sahalewar majalisar dattawan ƙasar.

”Amma mu daga ɓangarenmu har yanzu, babu wata buƙata mai kama da haka da shugaban ƙasa ya aiko mana majalisa”, in ji shi.

Amma ya ce da zarar majalisar ta ƙare hutunta za ta gudanar da bincike kan wannan batu.

”Za mu gayyaci ministan tsaro da babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar, mu ji gaskiyar wannan zargi”, in ji shi.

Mene ne martanin Faransa?

Kawo yanzu dai Faransa ba ta ce komai ba ahukumance dangane da waɗanann zarge-zarge duk da cewa a baya ta sha musanta irin wadanna kamalami na shugaban mulkin sojin na Nijar.

Tun a watan Yulin 2023 ne dai Janar Tchiani ya jagoranci kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum tare da korar dakarun Farasansa daga Nijar.

Tun daga lokacin ne kuma aka riƙa samun zaman tankiya tsakanin Nijar ɗin da tsohuwar uwargijiyarta, Faransa, inda har Nijar ta nemi Faransa ta janye dakarunta daga ƙasar.

Buƙatar da Faransan ta amince da ita, inda ta janye dakarunta da ke yaƙi da ‘yanbindiga a fa din ƙasar.

BBCHAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *