Dadiyata: ‘A faɗa mana ko ɗan’uwanmu na da rai, mun gaji da kuka’

Spread the love

Ranar 30 ga watan Agusta, wadda a wannan karon ta kasance Juma’a, rana ce da aka ware a duniya domin tunawa da mutanen da aka sace, suka ɓata ɓat ba a jin ɗuriyarsu – musamman waɗanda jami’an gwamnati suka ɗauke.

Yawanci wannan na faruwa ne a inda ake fama da rikici to amma ƴan siyasa na amfni da hakan wajen rufe bakin abokan hamayya.

“Har yanzu hankalina a tashe yake idan na tuna daren da aka tafi da mijina. Har yanzu ƴata na tambaya ta yaushe babanta zai dawo gida, to amma ina ba ta haƙuri cewa zai dawo nan kusa saboda ya yi tafiya,” in ji Khadija Ahmed.

Haka dai take bayani tana zubar da hawaye, kan yadda aka tafi da mijinta, Abubakar Idris, da aka fi sani da Dadiyata, daga gida – shekara biyar da ta wuce.

Dadiyata malami ne a Jami’ar tarayya da ke Dutsinma, a jihar Katsina da ke Najeriya – kuma fitaccen mai suka ne ga wasu gwamnonin jihohi har ma da shugaban ƙasar a lokacin, inda yakan soke su a shafukan sada zumunta da muhawara.

Khadija ta ce mijin nata wanda a lokacin yake da shekara 30 da wani abu, ya dawo daga aiki ke nan daga wata ziyara da ya kai wani gari, inda ya dawo bayan ƙarfe 12 na dare, ranar 2 ga watan Agusta na 2019, a lokacin da aka sace shi.

“Ina zaune da ƴata ina jiran ya dawo gida, bayan da ya komo gida ina ganinsa ta taga lokacin da ya tsaya a cikin motarsa yana waya.

DANDALIN KANO FESTIVAL

“Daga nan kawai sai na ga wasu mutane a kusa da motarsa suna magana da shi. Sai hankalina ya tashi. Nan da nan na garzaya na kira makwafciyata. Lokacin da muka zo muka kira ƴansanda har sun tafi da shi,” in ji ta.

Daga wannan lokaci yau shekara biyar babu ɗuriyar Dadiyata ko motarsa, kuma babu wanda ya tuntuɓi iyalinsa domin karɓar kuɗin fansa. Ba su san ko yana da rai ko ya mutu ba.

Khadija na ƙoƙarin rarrashin babbar ƴarsu mai shekara 10, a yanzu, inda take faɗa mata cewa ta daina sauraron mutanen da suke ce mata babanta ba zai dawo ba, kuma tana cike da yaƙinin cewa har yanzu yana da rai.

Ta’addanci
Shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan’adam ta Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi ya ce galibi ana ɓatar da mutane ne bisa dalilai biyu – ko dai a rufe bakin masu suka ko kuma a sanya tsoro a zukatan wasu.

Wannan kuma matsala ce da yawanci ke faruwa a Syria da Sri Lanka da Sudan da Pakistan da Libya da kuma Najeriya, in ji Sanusi.

Ita ma ƙungiyar agaji ta Red Cross, duk da cewa ba ta da alƙaluma na yawan mutanen da suka ɓace, ta ce akwai kusan mutum 100,000 da suka ɓace a Mexico da Colombia da kuma ƙila dubbai a Iraqi.

Shugaban ƙungiyar Amnesty a Najeriya, ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Najeriya, a kan gaza samar da wata rajista ta yawan mutanen da aka ɓatar, da kuma gaza gudanar da bincike, hatta na mutanen da suke fitattu, kamar Dadiyata.

Wata ƙungiya da ba ta gwamnati ba mai suna Jire Dole Network of Victims, ta ɗora wa kanta ɗawainiyar adana alƙaluman yawan mutanen da suka ɓace – inda a shekara 11 da ta wuce take da sunayen mutum 25,000, kamar yadda wadda ta kafa ƙungiyar, Hamsatu Allamin ta bayyana.

Ta ce yawanci jami’an tsaro ne da sauran jami’an gwamnati ke ɓatar da mutanen. Ta ce ƙungiyar ta gano cewa sojoji ba su ma san yawan mutanen da suke riƙe da su ba, kuma ba su ma san yawan waɗanda suka mutu a tsare ba.

A watan Nuwamba Amnesty, ta shigar da ƙara a kotun ƙungiyar ECOWAS, a kan yadda take zargin Najeriya, da take haƙƙin ɗan’adam, ta hanyar barin sojoji su ɓatar da dubban mutane musamman a yankin kudu maso gabashin ƙasar, sannan kuma ta kasa gudanar da bincike na gaskiya.

Barazana
Iyalan Dadiyata ba su san wanda ya ɗauke shi ba, amma sun ce daman yana samun barazana daga ƴan siyasa na ɓangaren gwamnati.

“Akwai lokacin da sai da ya ɓuya tsawon kwana uku a gidan kawunmu, saboda barazanar da wasu ƴan siyasa ke masa cewa za a sace shi,” in ji ɗan’uwan Dadiyata, Usman Idris Usman.

Ya ƙara da cewa duk wasiƙar da suka aika wa shugabannin ƴansanda da hukumar DSS, ta neman taimakonsu, ba su ba su amsa ba, kuma ita ma gwamnati ta yi burus da su.

Usman ya ce, hatta gwamnonin jihohi ma sun ƙi sauraron su.

Su faɗa mana kawai idan yana da rai ko kuma ya rasu ba za mu iya ci gaba da zubar da hawaye fiye da yadda muka yi a baya ba,” in ji Usman.

Hukumar ƴansandan ciki ta DSS, ta musanta kama mutane har a daina jin ɗuriyarsu, inda kakakinta Peter Afunanya ya ce jami’ansu suna bin ƙa’idar doka wajen gudanar da aikinsu.

Kakakin ya ƙi yin magana a kan batun ɓatar Dadiya.

Matar Dadiyata, Khadija, ta ce ita dai har yanzu tana cike da fatan sake ganin mijinta da rai, shekara biyar bayan ɓatansa.

“Ina addu’ar Allah ya dawo da shi gida lami lafiya, wannan shi ne fata na kawai a rayuwa,” in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *