Jami’an tsaro a Najeriya sun kashe ‘yanfashin daji huɗu tare da yin nasarar ceto mutum 20 da suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar.
Kwamashinan tsaro a jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce lamarin ya faru ne a ƙananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da ke jihar.
Ya ce dakarun aikin tsaro na Operation Forest Sanity ne suka kai samame a Alawa da ke Birnin Gwari bayan bayanan sirri sun nuna ‘yanbindiga na kaiwa da kawowa kuma suka kashe biyu daga cikinsu.
“Sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 biyu, da harsasai, da babur uku, da kuma na’urar sadarwa ɗaya,” in ji shi cikin wata sanarwa.
A wani samamen daban, dakaru sun kai hari ƙauyen Nakwakina, “inda suka yi kwanton ɓauna a wata hanyar wucewar ‘yanta’adda, wanda ya jawo kashe biyu daga cikinsu sauran kuma suka gudu da raunuka”.
Bugu da ƙari a cewarsa, dakarun Operation Whirl Punch sun kai ɗauki tare da shan gaban wasu ‘yanbindiga da suka yi garkuwa da mutum 20 a ƙauyen Polewire, inda suka gudu suka bar mutanen bayan sun hangi jami’an tsaro.