Dakarun Kwastam sun kama bindigogi 844 a tashar ruwan jihar Ribas

Spread the love

Hukumar kwastam a Najeriya ta ce ta kama makamai da harsasai da aka yi yunƙurin shiga da su ƙasar ta tashar ruwan Onne da ke jihar Ribas a kudancin ƙasar.

Da yake ba da sanarwar a yau Litinin yayin taron manema labarai, shugaban hukumar Adewale Adeniyi ya ce dakarun hukumar sun yi nasarar kama makaman ne tun ranar 21 ga watan Yuni.

Ya ce bayan tattara bayanan sirri, dakarun sun lura da wata kwantena da ta fito daga ƙasar Turkiyya wadda ke ɗauke da bindiga 844 da kuma ƙunshin harsashi 112,500.

“An ƙunshe su ne a cikin ƙofofi, da kayan ɗaki, da kayan gyaran famfo, da jakunkunan leda, waɗanda aka biya wa kuɗin haraji na naira miliyan ₦4,171,710,000.00,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, a jiya Lahadi ma dakarun kwastam sun tare wasu kwantenoni takwas masu tsawon ƙafa 40 da aka yi niyyar kaiwa wani wurin ajiya daga tashar ta Onne.

“Suna ɗauke ne da kwalaben maganin tari 1,050,000, da ƙwayoyin Trodol Benzhexol 3,500,000, da dilar kayan gwanjo 720 da aka biya wa harajin naira miliyan ₦13,915,710,000.00.,” a cewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *