Dakarun sojin Najeriya sun ce sun kashe ‘yanbindiga biyu a jihar Kaduna

Spread the love

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta daƙile wani mummunan hari da ‘yanbindiga suka yi yunƙurin kaiwa a jihar Kaduna da ke arewacin ƙasar ta hanyar kashe biyu daga cikinsu.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Laraba ta ce bayan tattara bayanan sirri, ta yi nasarar yi wa mahara huɗu kwanton ɓauna ɗauke da makamai a yankin Kurmin Aja da ke ƙaramar hukumar Kagarko.

“Cikin ƙwarewa dakaru suka yi musu kwanton ɓauna ta hanyar buɗe musu wuta, inda nan take suka kashe biyu daga ciki yayin da sauran suka tsere da raunikan harbin bindiga,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa bayan fafatawar ne kuma aka gano bindigogi ƙirar AK-47 biyu, da ƙunshin harsasai 30, da babur biyu na ‘yanbindigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *