Wata dalibar Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya da ke Mubi, Jihar Adamawa ta kashe kanta sakamakon rabuwa da saurayinta.
Dalibar mai shekara 24 tana karatun aikin jarida ne a Kwalejin kuma tana aikin daukar horo ne a gidan talabijin na Adamawa (ATV) da ke Yola.
Dalibar wacce ’yar asalin Garkida Gombi ce, an tsinci gawarta ne a dakinta da ke unguwar Hayin Gada, a Karamar Hukumar Girei a jihar.
An dakatar da yin gwanjon kayan Mandela
Ana zargin ta sha guba ne sakamakon bakin cikin rabuwa da saurayinta.
Rahotanni sun bayyana cewa, saurayin Balami wanda malami ne a Jami’ar Modibbo Adama (MAU) ya bukaci su rabu, lamarin da ake ya sanya ta kashe kanta.
Kotun ƙoli za ta saka ranar yanke hukunci kan ƙarar Binani da Fintiri
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya ce mahaifin dalibar ya kawo musu kara kan lamarin.
Kakakin ya ce rundunar za ta yi bincike domin gano musabbabin mutuwar dalibar.