Gamayyar Dalibai yan asalin jahar Kano, sama da dubu ashirin da bakwai 27,000 wadanda suke karatunsu a jami’ar Bayero Kano, sun roki jami’ar ta Kara mi su lokacin biyan kudin makaranta sakamakon matsin tattalin arzikin da ake dama da shi a Nigeria.
Shugaban daliban yan asalin jahar Kano, na kasa Kwamared Isiyaku Aliyu Kanwa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake gana wa da Wakilin Idongari.ng, a birnin Kano.
Kwamared Isiyaku Aliyu, ya ce jami’ar ta sanya Ranar 14 ga watan Yuli 2024, a matsayin Ranar da za ta rufe shafin biyan kudin makarantar , kuma yanzu haka wadanda Suka iya biyan kudin ba Su Kai dalibai 1,000 ba.
Ya kuma Yi Kira ga gwamnatin kano da yan majalissar dokokin jahar da na tarayya harma da yan kasuwa , Su taimaka wa daliban domin fitar da Su daga wannan hali.
- Gwamna Buni ya dakatar da shugaban karamar hukumar saboda rashin da’a a Yobe
- Yadda Aka Yi Arangama Tsakanin ’Yan Daba Da Matasa A Masarautar Rano