Daliban Makarantar Allo 100 Sun Amfana Da Tallafin Gidauniyar Tsohon Akanta Ahmed Idris.

Spread the love

Gidauniyar tsohon akanta Janar na Nigeria, Ahmed Idris, Ajiyan Hausa Matawallen Turai,ta gwangwaje wa su daliban makarantar Allo dake garin Ketawa a karamar hukumar Gezawa Kano, da kayayyakin da za su yi amfani da su wajen tsaftace kansu a bukukuwan Karamar Sallah.

Babbar jami’ar gidauniyar,Hajiya Hadiza Bala Fagge, ce ta jagoranci rabon kayan da suka hada da Sabulun Wanka, Omo, Man Goge baki, Man shafawa da kuma Takalma.

Kamanin dalibai 100, ne suka amfana da tallafin gidauniyar ta Alhaji Ahmed Idris, don faran ta mu su wajen yin kwalliyar sallar kamar kowa.

Hajiya Hadiza Fagge, ta yi kira ga daliban su kasance ma su yin amfani da kayan tallafin da suka samu, ta hanyar da ta da ce.

Ta kuma yi fatan daliban za su sanya Ajiyan hausan Matawallen Turai, cikin addu’o’insu na yau da kullum.

Suma daliban da kuma malamansu sun bayyana farin cikinsu sakamakon wannan tagomashi da gidauniyar Alhaji Ahmed Idris, ta saba bayar wa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *