Dalilin da ya sa muke tsare da shugaban hukumar alhazai ta Najeriya – EFCC

Spread the love

Wata majiya mai karfi daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa, ta EFCC ta tabbatar wa BBC cewa hukumar na ci gaba da tsare, shugaban hukumar alhazan Najeriya, Jalal Arabi tare da sakataren hukumar Abdullahi Kontagora.

Ana zargin shugaban da yin sama da fadi da wani bangare na naira biliyan 90 da gwamnatin Najeriya ta ba hukumar a matsayin tallafi ga aikin hajjin 2024 da ya gabata.

Hukumar ta ce an gano kudin da yawansu ya zarta Riyal dubu 300 daga hannun shugaban da wasu manyan jami’an hukumar hajjin ta Najeriya.

EFCC ta kara da cewa bincikenta ya gano shugaban hukumar ya yi amfani da wani bangare na naira biliyan 90 din da gwamnatin Najeriya ta bai wa hukumar aikin hajjin a matsayin kudaden tallafi wajen biyan kansa da manyan jami’an kudaden da suka wuce kima.

Bayanan sun nuna cewa hukumar na neman bahasi ne game da yadda aka kashe naira biliyan 90 da gwamnatin tarayya ta bai wa NAHCON a matsayin tallafi ga mahajjatan Najeriya na 2024 da aka kammala a watan Yuli.

Kazalika, hukumar EFFCn ta ce a kasafin kudi na bana ainihin kudaden da aka warewa kwamishinoni da manyan daraktoci da ma’aikatan hukumar sun saba yadda suka tsara nasu tare da wawure kaso mafi yawa daga abin da aka kayyade ma kowanensu.

Majiyar ta EFCC ta kara da cewa ana zargin shugaban hukumar hajjin da ware wa kansa Riyal dubu hamsin a maimakon riyal dubu goma sha biyar da dari tara da shirin da tara da aka ware masa a hukumance, yayin da kwamishinonin hukumar uku da aka ware wa riyal dubu goma sha biyar da dari tara da ashirin da tara kowanensu sai ga shi an biya su riyal dubu arba’in.

Tun a ranar 30 ga watan Yuli ICPC ta gayyaci shugaban hukumar alhazan, Jalal Arabi, domin ya yi mata bayani game da yadda hukumar ta gudanar da aikin Hajjin da ya gabata.

Wata sanarwa daga hukumar ta ce an gayyace shi ne kawai bisa tsari kamar yadda hukumar ta saba yi duk bayan kowane aikin Hajji.

Tun da farko naira miliyan hudu da dubu dari tara ne hukumar ta tsayar a matsayin kuɗin kujerar zuwa aikin Hajjin da maniyyata za su biya, amma sai ta mayar da shi miliyan shida da dubu dari takwas tana mai ɗora alhakin kan karyewar darajar naira.

Bayanin ya kara da cewa an gano zunzurutun kudin da yawansu ya kai riyal miliyan takwas da dubu dari shida da sha hudu da aka cire daga cikin naira biliyan 90 da gwamnatin Najeriya ta bayar da aka canza su zuwa dalar Amurka inda suka kama dala miliyan sittin da biyu da dubu dari uku da bakwai da dari da sittin da hudu, da kuma aka saka su asusun ajiyar hukumar aikin hajjin da ke Saudiyya.

Kuma har yanzu ita kanta hukumar aikin hajjin ta kasa yin cikakken bayanin yadda sauran kudaden suka yi batan-dabo.

Ba ya ga biyan wasu kamfanoni da ke kasar Saudiyya miliyoyin kudaden da ba a san takamaiman aikin da suka yi ba.

A kwanan baya a hirarsa da BBC, Sanata Ibrahim Abdullahi Dan Baba, tsohon wakilin Sokoto ta Kudu a Majalisar Dattijai ta Najeriya ya ce irin badaƙalar da bincikensu ya gano game da ayyukan wasu daga cikin jami’an Nahcon, ya hada da badakalar kama wa mahajjata dakunan kwana a otal da ya wuce kima inda a maimakon a kama na kwana 40 sai a kama na kwana 90 domin a saka wasu daga baya a yi kashe-mu-raba tsakanin NAHCON da masu otal-otal din.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *