Dalilin da ya sa yan Najeriya suka kwana cikin duhu ranar Litinin

Spread the love

Najeriya ta sake fuskantar katsewar wutar lantarki sakamakon lalacewar babban layin lantarki na ƙasar a ranar Litinin.

Layin ya lalace ne da misalin ƙarfe 7 na yamma, kamar yadda sanarwa daga kamfanin rarraba lantarki ta ƙasa (TCN) ya bayyana.

Lamarin ya jefa miliyoyin ‘yan ƙasar da kuma sana’o’insu cikin duhu.

Shi ma kamfanin rarraba hasken wutar lantarki reshen jihar Kano (KEDCO) ya nemi afuwar kwastomominsa kan abin da ya faru a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

“Muna bakin cikin sanar da ku cewa an samu ɗaukewar wuta ne sakamakon matsalar da aka samu a layin wuta na ƙasa,” kamar yadda shugaban sashen sadarwa na kamfanin Sani Bala ya bayyana.

Ya ce hakan ne ya janyo rashin rarraba wutar zuwa ga kwastomomi.

“Muna rokon al’umma da su yi hakuri yayin da muke ci gaba da aiki tukuru don shawo kan matsalar ta faru da kuma mayar da wutar lantarki yadda muka saba,” in ji shi.

Ya buƙaci mutane da su kula sosai wajen kare kai daga masu sata ko lalata wayoyin wutar lantarki.

BBCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *