Dalilina na jan hankalin Najeriya ta yi hattara da IMF – Jega

Spread the love

Tsohon shugaban hukumar zaɓe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta yi hattara da rungumar dukkan shawawarin da Asusun Lamuni na bayarwa, inda ya ce shawarwarin suna ƙunshe da wasu abubuwa da za su iya jefa ƙasashe masu tasowa cikin yanayi mara kyau.

A hirarsa da BBC Farfesa Jega ya ce lallai akwai alfanun da ke tattare da hulɗa da irin waɗannan cibiyoyin, sai dai ya ce ƙasashen da suke karɓar shawarwarin, kamar gwamnatin Najeriya, akwai buƙatar yin hattara, ka da hulɗar ta jefa ƙasar cikin matsin rayuwa da za a daɗe ba a fita ba.

“Tun a 1992 lokacin da nake jagorantar ƙungiyar ASUU asusun laminunin na duniya ya tattara ministoci na ilimi suka yi taro a Kenya, suka ce ai Najeriya ba ta buƙatar jami’o’i, suka ce karatun da ya kamata a yi shi ne abin da suke kira “technical education” wato ilimi na fasaha da ƙere-ƙere, ba wai ilimi mai zurfi irin na jami’a ba. Irin wannan shawara da gwamnatin can baya ta yi na cikin abubuwan da suka janyo mana taɓarɓarewar ilimi a halin yanzu,” in ji shi.

Jega ya ce akwai buƙatar a yi la’akari da cewa suna bayar da shawarwari ne game da abubuwan da suke ganin za su fi amfani a gare su ba wai ga ƙasashen masu tasowa ba.

Tsohon malamin jami’ar ya ƙara da cewa daga cikin ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta akwai rashin shugabanci nagari, inda ya ce tun da aka dawo tsarin dimokuraɗiyya, jam’iyyu ba su cika tsayar da ƴantakara da suka cancanta ba domin fuskantar ƙalubale.

“Mun san lokacin da aka yi wasu tsare-tsare na tsuke bakin aljihu da ake kira “Structural Adjustement Program”, waɗanda bankunan suka kawo mana tun wurin 1992, irin tsare-tsaren da suke kawowa, su ce gwamnati ta fitar da hannunta wurin inganta rayuwar jama’a ko ba su tallafi, sai dai komai a bar shi a kasuwa, kuma yadda kasuwa ta yi, haka za a yi.

Tun lokacin ne suke bayar da irin waɗannan shawarwari. Don haka muna kyautata zaton a Najeriya ma irin abun da suke faɗa ke nan yanzu.”

Da aka bayyana masa cewa IMF ta zare hannunta daga batun cire tallafin man fetur, Jega ya ce, “To Allahu ne mafi sani, amma dai an riga an san su, kuma an san abun da suka yi a baya kuma dabarun suna da yawa. Wani lokacin ƙeƙe da ƙeƙe za a yi, wani lokacin cikin hikima za su gabatar da abubuwa a zo a ɗauka daga baya su ce a’a ai ba haka. Ni dai cewa na yi a yi hattara,” in ji shi.

Mene ne IMF?

Asusun bayar da lamuni na duniya wato IMF wata ƙungiya ce ta duniya da ke da mambobi a ƙasashe 190 da suke aiki tare don ƙoƙarin daidaita tattalin arzikin duniya da aka ƙirƙiro daga taron Bretton Woods da aka yi a 1944 a Amurka.

Taron ya samu halartar wakilai daga ƙasashe 44 a lokacin yaƙin duniya na biyu da suka haɗa da Burtaniya da Amurka da kuma Tarayyar Soviet a lokacin.

Taron ya tattauna tsare-tsaren kuɗi bayan yaƙin, da suka haɗa da yadda za a kafa tsayayyen tsarin musayar kuɗi da kuma yadda za a biya domin sake farfado da tattalin arzikin Turai da suka durƙushe.

Daga baya aka kafa IMF da bankin duniya don cimma waɗannan manufofin.

Kowace ƙasa na iya neman shiga, muddin ta cika sharuɗan da ake buƙata.

Sun haɗa da bayar da bayanai game da tattalin arzikinta da kuma biyan kuɗi na zama mamba a ƙungiyar. Kowace ƙasa za ta bayar da gudummawa daidai ƙarfin arzikinta.

IMF na yin abubuwa guda uku don sa ido da kuma tallafawa tattalin arziki:

  • Bibiyar al’amuran tattalin arziki da na kuɗi. Yana sa ido kan yadda ƙasashe ke aiki da yiwuwar fuskantar barazana, kamar rikice-rikicen kasuwanci, kamar a Burtaniya – na rashin tabbas da ficewarta daga Tarayyar Turai ya haifar.
  • Bai wa mambobinta shawara kan yadda za su inganta tattalin arzikinsu.
  • Bayar da rance na ɗan gajeren lokaci da taimako ga ƙasashen da ke fama da matsaloli.

Ana samun rancen ne ta hanyar biyan kuɗi da masu son shiga ƙungiyar ke yi.

A shekarar 2018, Argentina ta samu rance mafi girma a tarihin IMF na dala biliyan 57.

IMF na iya bai wa mambobinta rancen kuɗi da ya kai adadin dala tiriliyan ɗaya.

Tallafin da IMF ke yi wa duniya

Yawancin lokaci ana kwatanta IMF a matsayin “mai ba da rancen taimako ta ƙarshe”. A lokacin rikice-rikice, ƙasashe na neman taimakon kuɗi a wajensa.

Masanin tattalin arziki na Jami’ar Harvard, Benjamin Friedman ya ce yana da wuya a auna tasirinsa saboda ba zai yiwu a san ko talLafinsa ya sanya abubuwa yin kyau ba ko “mafi muni”.

Duk da haka, wasu sun yaba da rawar da Asusun ke takawa na tallafa wa Mexico bayan da ta bayyana cewa ba za ta iya biyan basussukan da ake bin ta ba a farkon shekarun 1980.

A 2002, Brazil ta samu rance daga IMF don gujewa gazawa kan basussukan ta.

Daga baya gwamnati ta samu damar farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar cikin sauri, kuma ta biya dukkan basussukan da ke kanta shekara biyu kafin lokacin da aka tsara.

A ɓangare sukar da ake yi wa IMF kuwa, ana sukar sharuɗɗan da IMF ke ɗora wa ƙasashen da take bai wa rancen kuɗi a wasu lokuta da cewa suna da tsauri.

Waɗannan sun haɗa da tilastawa ƙasashe rage rancen da gwamnati ke karɓa da yanke harajin kamfanoni da buɗe tattalin arzikinsu ga masu zuba jarin na ƙasashen waje.

Girka ita ce inda rikicin hada-hadar kuɗi na Tarayyar Turai ya fara a 2009, kuma ita ce ƙasa da ta fi fama da matsalar tattalin arzikin.

Masu sukar sun ce manufar tsuke bakin aljihun da IMF ta dage Girka ta bi – da nufin ganin gwamnati ta karɓo rance – ta wuce gona da iri kuma ta lalata tattalin arzikinta da al’ummarta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *