Dan Majalissar Tarayya  Gwarzo Da Kabo Ya Kaddamar Da Tallafin Abinci Ga Mutane 10,000 A Mazabarsa.

Spread the love

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo.

Dan majalissar mai wakiltar Gwarzo da Kabo a zauren majalissar tarayya Hon. Abdullahi muazu baban gandu ya kaddamar da rabon tallafin abinci ga mabukata da masu karamin karfi harsu 10,000 a kananan hukumomin don ragewa Alumma radadin matsin rayuwa da alumma suka tsinci kansu ciki.

Bada tallafin ya gudana a ranar lahadi 17 ga watan maris na shekarar da muke ciki a babban dakin ajiya na karamar Hukumar Gwarzo.

Hon. Abdullahi muazu yace ” hakika babu lokacin da yadace mutallafi Alumma musanman mu yansiyasa da dukkanin wanda Allah ya hore masa face a wannan yanayi na matsi da fatara da ake fama dashi kuma muna cikin wata mai falala wato watan ramadan hakika mutane nada bukatar a tallafesu a wannan lokaci, tabbas yazama dole muyabawa jagororin mu musamman mai girma ministan gidaje da raya burane Eng. Abdullahi Tijjani Muhammad Gwarzo ruwa Baba da tshon kwamishinan kananan hukumomin jihar kano Hon. Murtala sule Garo da sauran jagororinmu bisa goyan bayan da suke bamu wajen gudanar da irin wadannan aikace aikace.

Sojojin Najeriya sun kashe ƴan bindiga a Kaduna da Katsina

Gwamnatin Nijar Ta Yanke Hulɗar Soji Da Amurka

Daga karshe Hon. Baban Gandu yayi kiraga dukkanin wanda ya rabuta da wanan tagomashi da yayi amfani dashi ta hanyar data dace dubada anbayar da tallafin ne badan komai sai domin ayi amfani dashi ba domin a sayar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *