Danbarwar Masarautar Kano: Ribadu ya yi barazanar gurfanar da mataimakin gwamnan Kano a Kotu

Spread the love

Babban mai bai wa shugaban NAjeriya shwar kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya yi barazanar gurfanar da mataimakin gwamnan Kano kwamared Aminu Abdulsalam a gaban kotu bisa zargin ɓata masa suna.

A ranar Asabar ne mataimakin gwamnan ya zargi Nuhu Ribadu ya shirya mayar da Alhaji Aminu Ado Bayero, zuwa Kano bayan gwamnan jihar ya sanar da matakin tuɓe shi.

Aminu Abdulsalam, ya zargi Nuhu Ribadun da samar wa Alhaji Aminu Ado Bayero jirage guda biyu domin su kai shi Kano.

To sai dai tun a jiyan Nuhu Ribadu ya musanta zargin kamar yadda mai magana da yawunsa ya shaida wa BBC.

A cikin wata wasiƙa da lauyoyinsa suka aike wa mataimakin gwamnan sun buƙace shi ya nemi afuwar Ribadun cikin sa’o’i 24.

Lauyoyin sun kuma buƙaci mataimakin ya fito ya nemi afuwar Ribadun a cikin manyan jaridun ƙasar biyar da fitattun kafafen sada zumunta ko kuma su gurfanar da shi a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *