Dangote ya gode wa Tinubu kan ƙwarin gwiwar da ya samu na fara aiki matatarsa

Spread the love

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya miƙa saƙon godiyarsa ga shugaban Najeriya Bola Tinubu kan goyon bayan da ƙwarin gwiwa da kuma shawarwarin ya ba shi wajen fara aikin matatar man fetur ɗin da ya gina.

A ranar Juma’a ne matatar tara aikin tace iskar gas da kuma man jirgi.

Matatar da ta laƙume dala biliyan 19 wajen aikin gina ta za ta riƙa tace ganga 650,000 a kowace rana, za ta yi ƙoƙarin kawar da matsalar karanin man fetur da Najeriya ke fuskanta.

TALLA

Dangote ya kuma gode wa kamfanin mai na ƙasar NNPC da hukummomin kula da sarrafa albarkatun man fetur na ƙasar NUPRC da NMDPRA da kuma ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suka ba shi don tabbatar da fara aikin matatar.

Yayin da yake bayyana matatar a matsayin ”mai sauya lamura”, Dangote ya ce a yanzu matatar za ta riƙa tace ganga 350,000 a kowace rana kafin baya baya ta riƙa tace abin da aka tsara tun farko.

Matatar ta tara gangar mai miliyan shida kafin ta fara aikin tacewar.

Sabuwar matatar- wadda aka kwashe kusan shekara bakwai ana ginata – za ta iya loda wa manyan motocin dakon mai 2,900 a kowace rana.

Ana ganin fara aikin matatar zai taimaka matuƙa wajen wadata Najeriya da man fetur, har ma ta zama ƙasa mafi fitar da tataccen man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *