Dangote ya karya farashin man fetur

Spread the love

Matatar mai ta Dangote ta karya farashin man fetur daga Naira 950 zuwa Naira 890 kan kowace lita a yammacin wannan Asabar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban sashin yada labarai da hulda da jama’a na kamfanin Anthony Chiejina ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai.

Sanarwar da matatar man ta Dangote ta fitar ta ce sabon farashin zai soma aiki ne daga yammacin wannan Asabar.

Sanarwar ta ce kamfanin ya rage farashin man ne sakamakon yadda aka sami saukin makamashi a kasuwar duniya, da kuma yadda farashin danyan mai ya sauka.

Kamfanin ya bukaci yan kasuwar dake sayan kayansu da su tabbatar sun rage farashin don al’umman Nigeria su amfana da saukin domin inganta rayuwarsu kamar yadda shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yake fata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *