Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya koka kan ƙarin kuɗin ruwa da babban bankin ƙasar CBN ya yi da kusan kashi 30 cikin 100.
Yayin da yake jawabi a taron kwana uku da ƙungiyar masu masana’atu ta ƙasar ta shirya a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja, Aliko Dangote ya ce ƙarin kuɗin ruwar zai kawo cikas ga ayyukan ci gaba tare da rage ayyukan yi a ƙasar.
Hamshaƙin attajirin na Afirka ya ce a wannan matsayi na kuɗin ruwa da ake ciki, masana’antu ba za su iya samar da ayyukan yi ko wani ci gaba da zai inganta harkokin tattalin arziki ba.
Babban bankin ƙasar ne ya samar da ƙarin kuɗin ruwan a lokacin zaman kwamitinsa kan tsare-tsaren kuɗi daga kashi 24.75 zuwa 26.35
Gwamnan babban bankin ƙasar Olayemi Cardoso, ya ce an yi ƙarin ne ”domin magance matsalar hauhawar farashi da ƙasar ke fuskanta”.
A baya-bayan nan ne Bankin duniya ya gargaɗi CBN ɗin da cewa ƙarin kuɗin ruwa ba zai magance matsalar hauhawar farashi ba, maimakon haka yana iya kawo tarnaƙi wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasar.
Aliko Dangote ya ce abin da ya kamata gwamnati ta yi shi ne ta samar da sabbin tsare-tsare da za su kare masana’atun cikin gida, ta hanyar samar musu da kyakkyawan yanayin da za su inganta kasuwancinsu.
”Babu wanda zai samar da ayyuka da wannan tsari na ƙarin kashi 26 a matsayin kuɗin ruwa, babu ci gaban da za a samu a haka”, in ji hamshaƙin attajirin.