Dangote zai haɗa kai da kamfanin MRS don sayar da litar fetur naira 935

Spread the love

 

Matatar mai ta Dangote a Najeriya ta ce za ta haɗa hannu da kamfanin mai na MRS domin sayar da litar man fetur a kan kuɗi naira 935 a gidajen mansa da ke faɗin ƙasar.

 

Cikin wata sanarwa da kamfanin Dangoten ya fitar ranar Asabar, ya ce shugaban kamfanin Aliko Dangote ya yaba wa shugaban Najeriya Bola Tinbu kan matakin da ya ɗauka na sayar wa matatarsa ɗanyen mai da kuɗin naira, wanda ya ce ya yi tasiri kan tattalin arzikin ƙasar.

 

Dangote ya ce hakan ya kuma taimaka wajen samun raguwar kuɗin man fetur a cikin ƙasar.

“Domin kawo wa ‘yan Najeriya sauƙi, a baya Dangote ya rage farashin mai daga 970 zuwa 899.50 ga masu sarin man a matatarsa, kuma domin tabbatar da ragin ya isa kan masu amfani da man, mun cimma yarjejeniya da kamfanin MRS domin sayar da man kan naira 935 a gidanjen mansa,” kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

Matakin na zuwa ne bayan da babban kamfanin mai na ƙasar NNPCL ya sanar da rage farashin man zuwa ƙasa da naira 1,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *