Farashin kuɗin intanet na bitcoin ya tashi zuwa sama da dala $80,000 (fan 60,000) a karon farko, bayan nasarar da Donald Trump ya yi a zaɓen shugabancin Amurka.
Hakan na faruwa ne kuma yayin da ‘yan jam’iyyar Republican ke shirin kame jagorancin majalisar wakilan ƙasar, bayan tuni ta kame jagoranci a majalisar dattawa.
Yayin da yake yaƙin neman zaɓe, shugaban mai jiran gado ya ci alwashin mayar da Amurka “babban birni na kuɗin kirifto”.
Yanzu kuma sai ga shi darajar kuɗin intanet mafi girma ta tashi da sama da kashi 80 cikin 100 a shekarar nan.
Sauran kuɗaɗen kirifto, ciki har da dogecoin – wanda attajirin duniya kuma mai goyon bayan Trump, Elon Musk, ya yi ta tallatawa – na samun tagomashi.
Kafin zaɓen, Trump ya ce zai ƙirƙiri rumubun rumbun bitcoin kuma ya taimaka wa cibiyoyin kuɗi da ke da alaƙa da intanet – inda ake hasashen zai janye dokokin taƙaita amfani da kirifto.
Trump ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da zai fara yi shi ne korar shugaban hukumar saka ido kan hada-hadar kuɗi ta Securities and Exchange Commission (SEC), Gary Gensler.
Mista Gensler, wanda Joe Biden ya naɗa a 2021, shi ne ya jagoranci yaƙi da kuɗaɗen kirifto a Amurka.
“Idan gwamnatin Trump ta cire dokokin amfani da kirifto, da wuya a ce babu ƙarfafa gwiwa a harkar nan,” a cewar Matt Simpson, wani mai sharhi a StoneX Financial, yana mai cewa hakan zai iya ɗaga darajar bitcoin zuwa $100,000.
Aniyar Trump da ta ƙunshi rage haraji, da rage dokoki kan harkoki, ya jawo ƙarin zuba jari a wasu harkokin tun bayan nasarar tasa.
Idan har jam’iyyarsa ta yi nasarar kame duka majalisun Amurka biyu, to za su iya samun damar ciyar da ƙudirin gwamnatinsa gaba ta hanyar amincewa da dokoki game da kowane ɓangare na kasuwanci.
BBCH